Tuesday, May 21, 2019
BAKANDAMIYAR GUMURZU kashi na biyu 2

Home BAKANDAMIYAR GUMURZU kashi na biyu 2


BAKANDAMIYAR GUMURZU
kashi na biyu 2
Littafin Umar Abdulhadi Mati


KADAN DAGA CIKI


[post_ads] Yayin da sadauki dalƙus da jarumi saljam suka karewa kansu kallo tsaf kowanne na tunanin yadda zaiyi ya cutar da abokin gwaminsa ba'a jima ba suka fara zagaya juna yaddakasan an tsikare su a tare suka ɗaga makamansu suka afkawa juna suna masu kaiwa junansu sara da suka cikin baki zafinnama yadda kasan jikinsu ba na jini da tsoka bane wohoho!! Hakika wanda ya iya ya huta, babban goro sai magogin karfe gani yadda suke safkewa junansu azabar yaki ce tasa filin gaba daya ya dau shewa da tafi kowanne yana kiran sunan gwaninsa yana kodashi hakika su sadauki dalƙus da jarumi saljam sun cika jarumai wanda suka tumbatsa a fagen fama domin kowanne daga cikinsu ya himma tu da safkewa abokin karawarsa masifar yaki haka suka wanzu har tsawon sa'a hudu amma ga yan kallo kamar yanzu ma aka fara domin su wanan yakin yana nishadantar dasu sosai domin jarumtace ta hadu da sadaukantaka abinda ya ba jama'a mamaki shine ganin salon yakinsu da zafinnamansu yaxo daya yadda kasan malami daya ya koya musu yaki a haka suka wanzu har saida makamansu suka lalace ganin haka yasa suka rabu kowanne daga cikinsu yaja da baya yana mai maida numfashi saljam ne ya fara watsar da takobinsa da garkuwarsa domin sun jima da lalacewa sana ya fuskanci dalƙus yana mai dunƙule hannunsa hade da yin [post_ads] murmushin mugunta sana ya bude baki karo na farko yace da dalƙus tunda salon yakinmu yazo daya kuma makaman yakinmu sun lalace me zai hana mugwada "yar ƙashi nan take dalƙus shima yayi jifa da tagwayen addunan dake hannunsa hade da yin murmushi na yadda da kai "hm inda ba kasa ai nan ake gardamar kokowa cewar dalƙus nan take shima ya fuskanci saljam yana mai duƙule hannunsa lokaci daya sukayi kururuwa suka afakawa junansu suka wanxu suna mai kaiwa juna duka kafa da hannu lokacinne fa hankalin "yan kallo ya tashi domin ganin yadda suke jibgar junansu yadda kasan jikinsu ba na jini da tsoka bane babu alamun sassauci a tare dasu kowanne burinsa ya lahanta dan'uwansa kafin kace mai tuni sun hadawa junansu jini da majina da wuya tayi wuya gumu yayi gumu da kansu suka rabu suka ja da baya suna mai kallon juna kowanne daga cikinsu yana mai tunanin yadda zai illata dan uwansa kamar an tsikaresu suka fallo da gudu saida ya rage baifi taku ukku su haduba sai dalƙus ya daka tsalle ya tsallake saljam duk tsawonsa kafin ya juyone yaji


DOMIN DOWNLOAD NA LITTAFIN SAI KU DANNA 👇👇👇👇👇👇👇

[post_ads]

Share this


Author: verified_user

Talented Aurthor, blogger in fashion and YouTuber in habits, I am living in keffin Magaji Dan Yamusa, Nasarawa state Nigeria, I am specialist at any kind of webdesign,webdevelopment, graphics designer and video editing I can make inpossible to possible with my laptop

0 Comments: