RIBAR BIYAYYA by sawwama page 4,5,6,7,8,9,10 - HAUSA EBOOKS -->

HAUSA EBOOKS

NQNia.blogspot.com Is a Premium Template Sharing Blog

RIBAR BIYAYYA๐Ÿ’–By Sawwama A. Page 4.A zaune ya sami hajiyar cikin shiga ta alfarma kyakyawar macece wace tsufarta ya b'uya cikin jin dad'i da kyan jiki fuskanta na d'auke da manyan idanuwa da dogon hamcim da take yawan hurashi hakan yasa hancin ya zauna haka a bud'e saboda sabon da akayiwa hancin saboda masifa.

K'arasawa yayi ya zauna a k'asan kujerar da take ya d'ora kansa a bisa cinyanta ita kuma tajiye jaridar da tun da ya shigo ta daina karantawa ta d'ora hannunta a kanshi tare da fad'in ya "akayine babana me kawun naka ya fad'a maka ina fatan ba matsalar wancan shed'aniyar yarinyan can da uwarsu ta gama zugeta bane?" Turo baki yayi cike da shagwab'a irin na tabb'arrun yaran nan yace "kai hajiyata ni wanne toh zan ansa sai jero min tambayoyi kike?" Shafa kanshi tayi tace toh yi min bayani a nutse" d'ago kanshi yayi ya sake turo baki yana wani shagwabewa yace " toh ba tace wai ni nayi mata yaro ba kuma ni d'an k'auyene kum...." A harzuk'e ta katseshi da fad'in a haifeka a turai ka taso a turai sannan ta kalleka tace maka d'an k'auye kuma ina batun yaranta yake a nan tunda ka mallaki hankalinka gaka da iliminka da sana'arka banda ka dagewa koyarwan nan daka sa kanka ga kamfaninka da mahaifinka ya bar maka amma a dubeka ace maka yaro d'an k'auye saboda tab'ewa da rashin rabo?" Ajiyar zuciya ya sauke yana murmushi dan shi d'in me yawan murmushi ne yace kin san 'yan Jos d'in nan in kana Bauchi ko wani gari na Hausa fulani d'aukanka suke d'an k'auye bagidaje saboda mu bamu d'auki d'abi'ar yahudawa ta sanya tufafi me nuna tsaraici da rashin sanin hakkin gabb'an jikin d'an adam kuma maganan yaranta tabbas ni d'in yaro ne shi ya sa kawu nema min mata k'aramar yarinya daidai ni...." Cikin k'araji ta kuma fad'in " me kake shirin gaya min in na fahimceka so kake kace min wancan k'abilar taci nasara a kanmu a karo na biyu kenan ta samu ta auri d'an uwana a b'agas sannan yanzu ta nemi hanamu had'a zumunci shi kuma wancan sallamamen sai biye mata yake yi har da wai ya samo maka mata a wani wajen" fuskantanta ya kuma yi da kyau yace " bafa a wani wajen ya sama min mata ba 'yar wajen sa d'ayar fatima ya bani." Hmm ta sauke ajiyar zuciya ba tare da tace komi ba dan ita gani kawai take an raina musu wayo ganin tayi shiru yasa ya cigaba da fad'in " shi yasa nake so kije ki sameshi a bar maganan nan da zuwa wasu 'yan shekaru dan ni ganin k'ak'antar yarinyan nake a bari zuwa ta gama secondary nima kafin nan na d'ora karatuna sai a ga abinda Allah yayi" yayi shiru ya zuba mata idanu yana me addu'ar Allah yasa ta yarda da hakan hikimarsa tayi hakan shine watak'ila in aka bar maganan zuwa wasu shekarun la Allah su daidaita ko kuma kowa ya had'u da abokin rayuwarsa a gaba danshi sam son da yake yiwa yarinyan na 'yan uwantaka ne toh ya ma zai iya mata wani so bayan nan yarinyan da take 'yar mitstsiya baya tunanin ko nono ta ajiye a k'irjinta, sai dai ina adu'arsa bata ci ba dan bud'en bakin hajiyar tasa sai cewa tayi " lallai kuwa Hauwa taci riba akaina ai haka take so uwar tasu dabarar ta kenan ai kaga itama wancan d'in in ta k'ara girma sai a hure mata kunne watak'ila ma ta nemi had'ata da wani birom d'in ko wani k'abilan nan cikin jos d'in ba dai aurene bata so y'ay'anta suyi a zuriyarmu ba ai kaman anyi an gama dan bazan yarda a wani d'au lokaci ba za ayi abinnan duk da ba wani son wancan yarinyan mai kama da zuriyar masu k'ananan ido nake ba dan yarinyan akwai falli in tace zata zo ta min halin uwarsu ni casa shegiya zanyi."

Rintse idanu yayi ya mik'e ya fice a palon ba tare da yace mata komi shi bai san ranan da hajiyarsa zata daina masifar ba gaira ba dalili ba ko me mamansu fatee tayi mata oho to ita fatin me ta tab'a mata dan dai kawai itace shugaban masifafun Bauchi tsaki yaja yana since kayan shi dan shiga ya watsa ruwa.

๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–

Zaune suke a gaban mahaifansu inda baba yake magana da adeeja ya fara " ki gayawa shi manemin naki kwanaki 14 na bashi ya turo magabatanshi in ba haka ba kar in k'ara ganin ya kiraki a waya dan ni ban son harkar yaudara nayi bincike a kansa duk abinda kika fad'awa mamar taku a kanshi gaske ne saboda haka yanzu shi mike jira a tsai da magana nayi waya da hajiya zata zo ke kuma" ya juya kan fatima " na san ke kam d'iyace me biyayya na san komi na yanke a kanki ba za ki ban kunya ba shi yasa na yanke shawara akanki ba tare da ko mamanki nayi shawara ba saboda na san na isa dake" gabanta ne yake lugude yayin da ita adeejan duk ta muzanta dan ta san gugar zana yake mata duk da bata san me yake shiri faruwa da y'ar uwarta ba.

A cikin tsakiyar kanta taji yana cewa " na ba da auranki ga d'an uwanki sagiru" a firgice ta d'ago da kai sai kuma ta mayar da kanta k'asa tuno irin yabon da mahaifinsu ya mata kafin ya furta musu zance adeeja kam jin zancen tayi banbarakwai sai abin ma yaso bata dariya har sai da ta murmusa wai dole ne sai ya auri 'yar gidansu" baba ne ya cigaba da yiwa fatima nasiha ita kam sai hawaye take wanda ta rasa dalilin zubar hawayen dan ita baza tace tana k'in yayansun ba amma ita sam bata mishi soyayyan aure kukanta ba zai rasa nasaba da ya makomar karatunta yake ba wai shin ita dukka dukka shekarunta nawa da za a kinkimo mata magana aure anya baba na lissafin shekarunsu kuwa? Haka tayi ta sak'e saj'e har baban ya gama maganarsa ya sa musu albarka ya fice.

Mama ce ta matso kusa da ita tare da dafa ta d'ago kanta tayi wasu hawayen na zubo mata hannu maman ta sa tana goge mata hawayen tare da furta " Saahyu ra pfenda daramo( kiyi shiru kiyi abinda babanki yace) kinga in kika k'i y'an uwanku ni zasu zarga suce na hanaku aure a zuriyarsu a gabanki ranan hajiya ta kirani a waya tace ko nak'i ko na so ku yaransu ne kuma dole suyi iko daku dan basa yiwa yaransu auran dolene da ba abinda zai hana baba karami ya auri adeeja sai kace nice na hana adeeja ta aureshi kece yanzu zaki wankeni ki daure ki auri zab'in su zaki ji dad'i wata rana kinji" fad'awa jikinta tayi tana kuka tana fad'in ni ba wai bana so bane is just too early kaman kuna manta shekaruna i am just 15 years for goodness sake mah ko ina fulani i am not living like one is high time a daina wannan auran wurin(shekaruna 15 fa dan Allah ko da nake fulani ai bana rayuwa kamar bafulatana lokaci yayi da za a daina auran wuri)" gyad'a kai maman tayi tace " dagani har ke bamu da choice a gabanki yace baiyi shawara dani ba ya zartar da hukunci sai mu zuba musu ido Allah yayj zab'i ke dai ki daure ki bisu zaki ji dad'i ni na tabbatar miki da haka duk wanda yaji maganan iyayenshi ba ya tab'ewa zaki ci *ribar biyayya"* kad'a kai tayi tace" na miki alk'awarin ni kuma zan muku biyayya ko dan in wankeki a wajensu" murmushi mama tayi tace na gode 'yata Dagwi an nonwo wen homa neimo niraho (Allah ya miki albarka ya sa kema yaranki su biki) ameeen.

SAWWAMA QAWWAMA๐Ÿ˜˜
๐Ÿ’–RIBAR BIYAYYA๐Ÿ’–By Sawwama A. Page 5.Hajiya tazo tare da baffannin su da kuma yayyun sageer da suke gari maneman auran adeeja sun zo an tsai da aure wata biyu dan baba ya rantse ba zata kuma yi mishi shekara a gida ba tunda ita bata jin magana taje can ta k'arata in mijin yaso ya mai da ita makaranta. Sageer da fatima kuma an tsai da magana da zarar ta gama jss3 bayan sallan azumi kenan hakan ya kawo cecekuce a cikin anguwa da dangin mama inda ake ganin an shiga hakkkin yaran har wani wan maman ke barazanan maka su a kotu sai da mama da ngo suka yi jan ido tukun wanda hakan bai tsirar da maman daga shan zagin hajiya ba tattas ta wanketa wankin babban bargo.

Bayan tafiyarsu hajiyar adeeja ta shigo d'akin inda ta tarar da teema na ninke kayan da ta wanke musu ( dan tunda taji su hajiyar zasu zo ta gudu daga gidan kar ta sauke mata kwandan bala'in tak'i d'anta) dariya ta kwashe dashi tace "su amarya manya tare da angon aka zo ne banga kina farin ciki ba 'ya mai biyayya ki zauna a kashe miki rayuwa wai ke zaki faranta ran iyayyenki toh bari in gaya miki ki shirya kamuwa da yoyon fitsari tunda kika zab'i aure a wannan shekarun kina samun cuta ya sakoki dan halin 'yan Bauchi kenan in bai sakeki ba ya k'aro aure another halinsu kenan ke kuma kin zama rajab ya tsufar da ke saboda nuk'urk'usa a daidai lokacin da nake shan love da hameed d'ina."

Bata kulata ba sai da tagama adana kayanta har da na adeejan tace " adda adeeja ni yanzu kin daina ban mamaki sai tsoro kin koma kamar ba musulma ba kin kasa yiwa iyayenki biyayya ni da nake k'ok'arin yi musu kina neman ki hure min kunne ta hanyan tsoratar dani wai kam kina tunawa da cewa mama kike sawa a matsala duk wani hali da kike yi? Ba abinda masifafiyar matar nan ke cewa da ya wuce kin zuqa kafirci a nonon uwarmu wanda ita mahaifiyar tamu ba a haifeta a kafirci ba sai dan kawai tana ansa suna yaren birom shikenan ake dangantata da kafirci kema kuma kina taimaka musu wajen b'llo da wasu halaye baki tsaya a iyakan k'in musu biyayya da tsoratani ba har mugun baki kike bina da shi a matsayinki na 'yar uwata wallahi ki kama girmanki tun kafin ya fad'i dan in ya fad'i ba abinda zai hanani hawa in tattakashi har da tsalle."

Shak'ota tayi tana nufin jibgarta mamansu ta shigo ta fizgeta a hannunta tace " kar ki yarda ki tab'a min yarinya ke in ba kya tausayina ita tana sona tana tausayina ace kece babba sannan kuma kece ba ki da hankali Allah ya wadaran halinki hadija" ta ja hannun fatima suka barwa adeeja d'akin. 

๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–

Asalinsu mutanen Bauchi ne malam salisu shine mahaifinsu yayinda inna sala itace mahaifiyarsu su biyu tak ne a wajen mahaifansu Hadiza itace babba ratan shekaru biyar ne tsakaninta da k'aninta mustapha suna k'anana iyayensu suka rasu sakamokan gini da ya fad'o musu sanadiyar ruwan sama da aka tsuga a lokacin yaran sunje gidan k'anin babansu baffa umaru. 

Dole rik'onsu ya koma wajen baffan nasu da fari matar baffan ta so gwada musu mugun rik'o kasancewar hadiza yarinya ce me shegen tsiwa da masifa yasa ta shafawa kanta lafiya hadiza na gama primary aka hankad'ata GGC kafin madaki inda ta bar k'aninta wajen matar baffa tana azabtar dashi shima yana wayo ya k'arbarwa kanshi 'yanci.

Ranan da hadiza ta gama aji uku ana speech and price ta lashe mafi yawan kyautuka cikin manyan bak'in da suka zo alhaji musa ya nuna yana sonta bada jimawa ba aka sha biki ta tare a gidanta inda take rik'e mishi da yaransa maza biyu da matarsa ta mutu ta bari.

Haihuwarta biyu duk maza salis da mustapha alhaji musa ya sami aiki a america suka tattara suka koma can ba yanda bata yi ta tafi da k'aninta ba baffansu yak'i yace baza a d'aurawa bawan Allah nauyin da ba nashi ba can ta haifi salamatu da sagir mai sunan baban mijinta.

Shi kuma mustapha bayan gama secondary d'inshi ya sami gurbin karatu a university of jos inda yake karantan mechanical engineering yana shekara ta uku aka kama wani da satan ansa aka mishi cune aka koreshi. Bai gayawa kowa ba ya kama kanikanci a gada biyu nan ya had'u da hauwa yarinya birom cikakkiyar musulma ce gaba da baya sai dai zuriyarsu na cakud'e da marasa sallah baffa ya shige mishi gaba aka yi aure yayarsa cr ta had'o mishi lefe daga can ta aiko baffa shi ya hana a gayawa hadiza k'abilar da mustapha ya jajub'o kasancewarta mai kishin yare da addini.

Dawowarsu nigeria kuwa ba k'aramin artabu akayi ba dan fushi tayi da k'anin nata sosai wai k'aninta ne da aure wata k'abila har da rabon y'ay'a biyu lokacin shekarun fatima bakwai lokacin ne tazo da dukka ya'yanta gidan mustapha zuwa sagir na farko kenan yana d'an yaronshi ba k'ara zuwa ba dan shekarar ya shiga jami'a b'angaren k'iyayyar da hadiza ke yiwa hawwa kuwa sai abinda ya yi gaba.
Wannan kenan.

SAWWAMA QAWWAMA๐Ÿ˜˜
๐Ÿ’–RIBAR BIYAYYA๐Ÿ’–

By Sawwama A. Page 6.
*Alhamdulillahi Ina mai mutukar nuna farin cikina hakika baka sanin masoyanka sai abu ya sameka na gode muku masoyana Ana mugun tare irin sosai din nan*
 _Na manta a dalilin mutuwar alh musa ne yasa haj hadiza_ baro us

***** ******* *****

An tsai da ranan auran adeeja watanni biyu kacal Dan baba ya dage bazata karasa makaranta ba tunda ita bata ji. 

Fatima da sagir kuma an yanke bayan sallan azumi dai dai da ta gama jss3 kenan watanni shida nan gaba kenan. 

Adeeja da hameed sunfi kowa farin ciki cikar burinsu duk da adeejan na tausayawa yar uwarta halin da ake shirin jefata na aure da wuri sannan ga masifaffiyar uwar miji ga neman iliminta da ake shirin datseshi, dan ita tana da tabbacin hameed bazai datse mata karatu ba Dan sun gama shawarta suna aure zata koma tunda term daya ta rasa. 

Sagir bai samu zuwa ya ga fatima ba kaman yanda aka tsara ba saboda yanayin koyarwarsa kasancewan ba a cikin gari yake aiki ba a wani private boarding school mallakin abokin abbansa yake koyarwan. 

Hajiya bata son wannan nanatacen koyarwan amma ya dage shi abinda yake so kenan yayunshi sun shawarce shi yayi lecturing tunda yana sha'awar koyarwan yace ba yamzu ba sai nan gaba yafi son ganin ya fara from the very ground suka ki yarda dole ya fara daga secondary school. 

Shi rashin samun zuwa jos ya mishi dadi Dan har ga Allah yana kunyan ya daga ido ya kalli yarinyan a maysayinshi wai na Wanda zai aureta haba! AI da kunya shi kanshi kunyan kanshi yake wai wannan tatsitsiyar yarinyan nan ne future wife dinshi inaaaaa ba zai taba iya nunawa wanda suka sanshi fatima a matsayin wacce zai aura ko matarsa ba. 

Hmmm in dalibansa suka ji KO suka gan ta a matsayin matarsa ba karamin dariya zasu sha ba a irin yanda yake daure musu (awwn he wince) mussamman shegun matan nan masu shegen naci yara kanana sai son soyayya ya datsen halshensa da hakoransa kiransu yara da yayi dan ya San sun fi so called fiancee dinshi shekaru da komi da komi na fannin sura. 
Bangaren fatima kam tafi baba karami fargaba da kunyan haduwa da shi mussaman in ta tuna sokoncin da take tayi a gabanshi da yanda take koda kyanshi da manyan idanunshi wani sa'in har rufe fuska take da tafukan hannunta KO in tana kwance ta tuno sai ta ja bargo ta rufu har kanta. 

A haka rayuwa ya tafi har wata biyun da aka diba na bikin adeeja ya cika inda aka sha biki aka Kai amarya hajiya tayi rawar ganin wajen had a Mata kayan daki ingantatu sai fatan ta zauna lafiya da kishiyarta da mijinta a rikkos. 

Duk kumbiye kumbiyen fatima da baba karami Allah ya kawo mu hutn second term dole baba karami ya dawo gida yayi shirin zuwa zance kuma dole fatima tayi shirin tarban ba konta.

Yana zaune a dining yana cin abincin hajiyarsa yayin da hajiyar ke zaune a babban Palo tare da babban dan mijinta da yazo daga America tunda shi aa can yayi auranshi duk da matarsa yar Nigeria CE amma haihuwar can girman can. 

Tasowa yayi daga dining din ya dawo Palo ya zauna tare dasu. 

Da kulawa hajiyar ta dubeshi tace "babana yaushe ne zuwa jos din? "
 Dan yamutsa fuska yayi yace "wai hajia dole sai naje ne ba bikin saura 4 months ba? "
 Rike baki tayi tace dole kai AI dole kaje babana saboda mu nunawa wancan da gaskenmu muke ba Zan Bari ta rabani dan uwana Ba, kuma itama yarinyan ba sake mata zaka yi ta raina ka ba dan naga kan na rawa kaman na uwarta. 

SAWWAMA QAWWAMA๐Ÿ˜˜
๐Ÿ’–RIBAR BIYAYYA๐Ÿ’–

By Sawwama A.

Page 7.

Dakin ya dau shiru na dan wasu sakonni kafin daga bisani alh ashiru baban yayansu baba karami ya katse shirun da fadin "wai ni kam hajiya ba anyi hadin nan dan a kara dankon zumunci bane?" Ba tare da ya bata daman amsawa ba ya cigaba da fadin " toh menene xaki ce kar ya sakewa yarinyan da zai aura fuska? Ba sai an sake fuskan bane za a samu fahimtan juna? Dan Allah.hajiya.ki daina barin abinda ke tsakaninku manya yana shafan mu yaranku.

Duk da itama matan uncle din ba wai ta miki wani abu bane,laifinta daya a wajenki dan ta kasance wata yare which is not her fault beside hajiyarmu hausa,fulani,jarawa birom,angas,yoruba igbo duk daya muke a wajen Allah kuma shi ya hallicemu kuma yana sonmu matsawar muka bi dokokinsa, hausa fulani bai fi birom ba ba wanda ya fi wani a wajen Allah sai wanda ya fi tsoronshi.

Ganin yanda take muzurai sarai ya san ya kunnota fushin nata ya motsa da sauri ya juya ga d'an uwanshi yace "kanina bari in baka wani hadith _akwai wani mutum ya taba zuwawa ma'aiki yace yah rasulillah ka min wasiya sai annabi yace masa kada kayi fushi_ sai da annabi ya nanata sau uku. Me yasa annabi ya mana wasiya da cewa kada muyi fishi saboda mafi yawan hasara dukka tana zuww da fushine. Kaga yana da kyau mu dinga controlling fishinmu.

Fuuuuuuu ta tashi ta shige d'aki dan ya riga ya daureta da sauri baba karami ya kankame dan uwanshi yace wallahi babban yaya kafi kowa iya zama da hajiya pls ku tattaro ku dawo nan.

Murmushinsu na manya yayi yace ba dai mu dawo ba kasan auntynka ba yarda zata yi da zaman nigeria ba amma zanyi kokari mu zo azumi har zuwa bikinka.

Murmushi kawai yayi.

Washegari da yamma baba karami ya shirya zuwa jos zuciyarsa cike da fargaban ya zai fusakanci fatima.

Tana zaune mama na tubke mata gashinta mara cika sai dan tsaho da yauki sosai tsawonshi a bisa dokin wuyanta ya tsaya injita tace komi nata kadan๐Ÿ˜œ wayar mama tayi ruri da sauri ta daga cike da ladabi ta gama ansa wayan kallon fatiman tayi tace "fatima maza tashi ki kimtsa baba karami na hanya ki share mishi dakin zauren

Dam gabanta ya fadi jiki a sanyaye ta mike ta canza kaya tunda dama tayi wanka ita abin wani iri yake mata toh wai kwalliya zata yi kai ah ah ai sai yaga zakewarta powder ta shafa da man baki.

Dakin zauren ta share ta saka turaren tsinke kafin ta koma daki zaman jiranshi tare da fargaba dama haka ake ji in za a zo wajenka zance kai ah ah duba da yanda adeeja ke rawar jiki in hameed zai zo tayi tq kalkale jikinta kenan jikinta har rawa yake sabanin ita da take jin mutuwar jiki da faduwar gaba.

Gabanta ne yayi mummunan faduwa jin muryarsa a tsakar gida suna gaisawa da mama, maman ce ta umarceshi da shiga dakin zauren shi kanshi jin sh wani iri yake shine da zuwa zance wajen fatima.

A hankali ta shiga dakin bakinta dauke da sallama ajiye tray din hannunta dake shake da abinci da na sha tayi kafin ta zauna tare da lankwashe kafa cikin rawar murya ta gaisheshi, bai amsa ba sai zuba mata ido yayi ganin duk yanda ta duburburce sai gyara zama take tana jan gyalenta da ta rufa a kanta wai yau fatima ce da kunyarsa ko da yake shima cike yake da kunyanta amma duk zai musu maganin abin

Bintoto ya furta cike da zolaya itama a hanzarce ta dago kanta jin sunan da yayi kiranta da shi ido ta zuba mishi ganin shu'umin murmushin da yake yi lokaci daya suka fashe da dariya dan tsagaitawa yayi da dariyarsa yace ko ba sunanki bane bintoto? Gyada kai tayi tana kokarin hadiye dariyarta tace " ah ah fatima zahra nake meye kuma wani bintoto?

Zo ki gani ya yafitota da hannu yana kokarin ciro wayarsa da dayan hannun youtube ya shiga ya searching abinda yake nema dariya tayi sosai dan ta manta ma matsayin da yq zo mata cikin dariya tacr Allah sai na nemi kaset din wakan nan na kalla.

Murmushi yayi yana kallonta yaji dadi fa wancan tension din ya fita a tsakaninsu fatima ya kira sunamta a nitse dago kanta daga kallon wayan tayi tana mishimurmishi

Ajiyan zuciya ya sauke yana kimsa maganan da zai furta mata Allah yasa kar ta mishi munmunan fahimta ta fassara shi

SAWWAMA QAWWAMA๐Ÿ˜˜
๐Ÿ’–RIBAR BIYAYYA ๐Ÿ’–By Sawwama A.
Page 8.

"Fatima" ya kira sunanta akaro na biyu wanda hakan shi ya ankarar da ita ta nutsu.

Fatima kinga hukuncin Allah ko? Iyayyenmu sun yanke hukuncin aurar damu ga junan mu ba tare da la'akari da kankantan ki ba. Ina so ki cire duk wani fargaba a ranki na aurena ki dauka kaman in anyi auranmu zaki bar nan gidan na wasu yan shekaru ne ki tafi karatu bauchi, a lokacin da kika mallaki hankalinki sai muga abinsa hali zai yi a wannan gaban ne za mu yankewa kanmu hukunci kin fahimceni?

Gyada mishi kai tayi ba tare da ta fahimceshi din ba. Good yanzu ina so kisaki jikinki da ni mu cigaba da kasancewa kaman da kar mu bari abin nan ya taba dangantakar mu nan ma ansa mishi kawai tayi a hankali ya cigaba da janta da surutu kafin wani lokaci har ta saki jiki ta ffara biye mishi ta fara shiriritar na ta.

Sosai iyayyenta suka ji dadin ganin yanda suka saki jiki da juna suna harkokinsu a nasu zaton sun rungumi juna suna soyayyarsu ne sabanin su da suka manta ma wai za a musu aure tare.

Kwanan baba karami biyu a jos a kwanaki biyun nan shaquwarsu da juna ya kara habaka inda ya dinga daukanta suna zuwa outing ya bi ya mata siyaya ya so siya mata waya amma sai ya duba kankantata wa ma zata kira kawai sai ya sai mata mp me kyau da tsada yace asha jin kida da karatu dai, dariya kawai tayi haka ya musu sallama ya koma bauchi.

๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–

Akwana a tashi asarar me rai har su fatima sun gama exams an tsunduma cikin shirin biki ita kam kallon abin take kaman shirin film ko littafin hausa sai dai ina a zahiri ne kuma a kanta ne, mutanen anguwarsu ta alheri sun cigaba da cece kuce akan batun auren da suke kira child abuse sai dai wasu daga cikinsu basu yi mamaki ba kasancewar sun san fulani da auren wuri sai dai sunyi zaton ai tuni an daina wannan yayin a dauki yarinya da bata gama rika ba a kaiwa wani kato yayi ta sassaka sun manta su nasu ya'yan da basu wuce 15 years ba sun iya su bude ma wani kato kafa saboda naira dari da zasu sai plate of rice Allah shi kyauta amin.

Abin mamaki baya karewa duba da yanda adeeja take wani shige da fice a auren sune kan gaba sai wani iyayi take tayi kyau sosai tayi hasken amarci dama tafi fatima kyau nesa ba kusa ba dan ita manya idanu gareta kaman su baba karami sabanin fatima da nata ba manya bane amma a waje suke basu shga ciki ba dogon hancinsu daya da karamin bakinsu kuma ita tana da diri tunda ta zama cikakkiya budurwa sabanin fatima da nonon ma yanzu suke fitowa kuma da alama ba mai manyan nono bace dan adeeja na da shekarunta nononta ya fi na fatin.

Fatima bin kowa take da ido yanda ake ta hidima kaman bikin wata babbar budurwa bata san aure sunanshi aure ba adeeja ce ta shiga kan nan na rawa tace ke kuma amarya baki tashi kin shirya ba wai ina kayan fitan biki ne da hannu ta nuna mata kayan da baba ya bayar a dinka mata da sauri ta karasa tana dagawa juyowa tayi tana kallonta kafin daga bisani tace wai kina nufin kayan da baba karami ya kawo kenan tace ah ah baba ya kawo min su.

Zama tayi a gefen gadon inda fatima ke zaune tace wai duk kudin su yah sagir din nan bai baki kudin kayan fitar biki ba bai kuma kawo ba? Wannan wani irin bikine ko event daya ba fa ayi ba ban nombanshi tagumi fatiman ta zuba tace ni ban da ita ki kyaleshi mana wadannan sun isa wallahi.

Harara ta wurga mata tace anki a barshi shegiya ke kike mishi da sauki ashe ta fita ta karbo number dan rashin kunya ta kirashi yana kwance yana baccinshi wayarsa tayi ringing kaman ba zai dauka ba kasancewar bai san numbern ba amma nacin kiran yasa ya dauka cikin karadi tace kai yah sagir kaman ba zaka dauka ba adeeja ce.
Sai da gabansa ya fadi ya dake yace ah ah mamana ya kike ya mijinki? Lafiyanmu lau gani nayi har gobe daurin aure bangga kayan fitan bikin amaryar taka ba ga shi ban ga kun shirya mana wani biki ba. Dan duburburcewa yayj dan shi sam ya manta wai gobe zai zama ango kuma shi bai san ana wani kayan biki ba event kuwa shi wa ya aikeshi hada wani taro a ga aamrya kamar yar yaye.

Hello kana jina ta katse shi, yeah yeah ina jinki ai naga ana kawo akwatina yau suna bisa hanya ma kuma naga kaman akwai dinkakun kaya a ciki kin san ni ban san ya ake yi ba kuma bata gaya min ba event kuma ni ba wasu abokanai gareni ba ai da kun shirya na family.

Haka ne kam Allah ya sa akwai dinkakkun ayi hidima lafiya ta katse layin ajiyar zuciya ya sauke yana me jinjina karfin halin adeeja ko ni na jinjina rashin kunyanta kice ba kya son mutum ki kuma zo kina kara nuna mishi auranshi da kanwarki be dadaki da kasa ba Allah ya kyauta.

Mutane sun gigita da dimbin kayan da akayiwa fatima kaman na wata big girl under wears da lingering bra ubansu ko a wani nonon za a sa oho๐Ÿ˜

An daura aura an kai amarya gidanta dake cikin gidan hajiya a bauchi inda a daren hajiya ta hada mothers night aka ci aka sha aka watse aka bar amarya da angonta sai fatan Allah ya zaunar dasu lafiya su ci ribar yiwa iyayensu biyayya.
๐Ÿ’–RIBAR BIYAYYA๐Ÿ’–

By Sawwama A. Page 9.A hankali yake kutsa kai cikin sashin yana tafe yana tina kalamen mama a gareshi. _baba karami ga amanar fatima,yarinya ce karama da bata san komo ba dan Allah ka sa tausayi a zuciyarka kafin bukata_murmushi yayi a hankali me hakan ke nufi mama tana gani zai iya sauke buqatarsa akan fatima ne? 

A hankali ya tura kofar dakin da yafi tunanin tana ciki. A takure ya sameta tana bacci tana zaune a kasa ta daura kanta a kan gadon karasawa yayi ya dan tapping dinta a firgice ta farka kasancewan daman a tsorace take, tana ganin shine ta fashe da kuka tare da fadawa jikinshi.
Hannu yasa ya rungumota da kyau yana shafar bayanta yana fadin "shshshhhhh issokey yi hakuri nayi zaton sun barki a gefen hajiya ne da na shigo tuntuni ai sorry ko cikin sheshekan kuka tace yah sagir tsoro nayi ta ji ni kadai fa gidan ta min girma. Daga girarsa yayi daya wai gidan ya mata girma dakuna biyu ne fa wanda ko wanne ke da bathroom sai palo da kitchen ko dining area babu. Sorry my sister bazan kara barinki ke kadai ba kinji? Ta gyda mishi kai kinyi sallah kuwa tace ah ah na kasa tashi inje inyi ina ta jin tsoro
Yace ok ina zuwa drawer ya bude inda aka jera mata kayanta kayan bacci ya ciro riga da dogon wando sai hula da hijab ya miko mata yace tashi ki shiga kiyo wanka tare da alawla ina jiranki karban kayan tayi ta marairaice fuska tace yah sagir dan Allah kar ka fita ka barni murmushi yayi yace bazan fita ba turo dan bakinta tayi tace ka ma fita na san me zanyi in rama baba karami nima zan koma ce maka dariya yayi yace bazan fita ba yi maza kije kiyi.

Yana zaune a dakin har tayi wanka ta fito sanye da kayan da hijab bayan gidan ya shiga ya watsa ruwa tare da yin alawla tunanin yanda zai daura towel.ya fita yake yi idonshi ya sauka kan rigan wanka hamdala yayi ya saka har lokacim tana sallah kila shafa'i da wutiri take fita yayi a dakin ya shiga nashi da sauri ya fitar da kayaking barcinshi ya zira wando yana kokarin sa riga ta fado dakin kaman wanda aka koro da sauri ya karasa zira rigar yana fadin yi hakuri nima kinga shiryawa nazo yi zo muje ya riko hannunta suka fita palo inda ya ajiye ledar da yayunshi suka bashi dan shi sam bashi da abokai yayunshi ne abokansa da hajiyarsa.
Kitchen suka je suka dauko plate da cups suka koma dakin sallah yaja su yana tune da yanda yaah ashir ya dinga jadada mishi sallar nan duk da a kasan zuciyarshi ya sb bazai kusanceta ba amma ya kudurta yin sallan, bayan sun idar ne suka sha fresh milk da kajin da ya shigo da shi a daddafe saboda baccon dake fisgarsu.

Yau kwananta uku a gidan daki daya suke kwana saboda fitinanan tsoronta dan ko a jos bayan auren adeeja charity ke zuwa tayata kwana. Yau tun asuba ake tsuga ruwa bacci suka koma bayan sun yi sallah 
Bata tashi farkawa ba sai goma har lokacin ana yayyafi ga wani sanyi da ya sauko tura baki tayi ganin ita kadaice a dakin wanka tayi ta dauko wasu riga da wando na sanyi ta saka ta dauko hulan sanyi ta saka shi har lokacin bata daina jin sanyin ba a fili tace kai sai kace muna jos palon ta fito tana goga tafukan hannunta yana zaune sanye cikin dogom wandon track suit da armless riga hannunshi rike da cup yana sham tea.
Zama tayi a one sitter tana ciggaba da goga hannunta tare da hura iskan bakinta me dumi "yah sageer ina kwana? An tashi lafia ,ya sanyi? Gira daya ya daga yace "wai irin wannan dogon gaisuwa toh duk lafiya" dariya tayi tace da kyau, wai kai kam baka jin sanyi ne ji yar rigar da kasaka? Kallon jikinshi yayi ya kalleta yace kenda kika tila wannan uban kayan ma baki fini jin dumi ba. Gyada kai tayi tana cusa hannunta tsakanin cinyanta tace Allah sai kace watan sha biyu ko watan daya a jos.
Ganin yanda take takurewa ya sa ya mika mata hannu yace zoki ji dumi tashi tayi ta karasa ya sata a jikinshi yace b abinda ya kai body contact saurin kawar da sanyi ita dai gabanta sai lugude yake dan ko da suke kwana daki daya bai cika kai hannunshi jikinta ba sai da dalili.
Sunyi kusan five minute a haka wani tunanine ta ziyarci kwakwalwanshi yace jeki hada tea kizo zamuyi magana jikinta a sanyaye ta tashi ta hada tea din ta dawo.
Sai da ta gama ya fuskaceta yace fatee kin san na taba gaya miki zamu yi zama ne ba irin zama na aure sai dai zama na yaya da kanwa ta gyada kai yace good nan da kwanki goma sha makarntar da nake koyarwa zasu koma hutu kuma tare zamu tafi sai dai ke a mattsayin daliba zaki kuma kanwata dan haka.nace musu ko da wasa ban yarda sabo yasa kiceqa wata wai ni mijinki bane mu yan uwan junane har abada kin fahimta? Nan ma gyada kan tayi kaman kadangaruwa yage yawwa bintoto dariya tayi tace aha baba karami shima dariyan ya tayata yace zaki sani ba dai kin rainani ba hannayenta ta hada tace ah ah ba raina yayana ba.

Cikin kwanaki bakwai wata shakuwa ce ta shiga tsakanin baba karami da fatima kasancewarshi mutum mai saukin hali ba girman kai a tattarre da shi haka zasu yi ta wasan guje gujensu a dan palonsu ko su kunna waka ya riketa suyi ta rawa har rawan tuawa yake koya mata yana bata labarin lokacin da yake america da budurwarsa ta high school da wace yaje prom night da ita tayi tq dariya yayi mata alkawarin in har tayi kokari a makaranta wata rana zai je da ita.

Plate din abinci ne a gabanta ta tabe baki tana shirin kuka gefe daya baba karami ne ya hade rai kaman bai taba dariya ba zata iya rantsewa wannan shine karo na farko da ta gamshi a yanayin nan cikin kakkausar murya yace kin san Alllah sai kinci abincin nan dubeki ba ko auki kuma karatu zaki fara amma ba kya son cin abinci cikin shagwaba tace yah sagir kaifa ka cika min ciki da madarar shanu kuma ace sai na cinye abincin nan yana shirin daka mata tsawa dan yaga alama sai yayi da gaske salallamin hajiya ne ya katse shi tace tabdi lallai auta kace raino kawai aka bakaa kara karewa fatima kallo take yi sai yau ta kara ganin yarintarta yarinya ko nono bata da shi sanye take da gajeran wandon jeans da rigga mai dogon hannu ta kama gashinta in a pony tail stayle yarintarta ya fito kararaa takaici ne ya kumeta amma wallahi an cuci autanta "haba dole uwarta ta yarda a hada auran nan tunfa ta san rainon yarta za a mata kai baba karami rabu da ita kar ta ci abincin ba cikinta bane" shaggwab fuska yayi kaman bashi ke mazurai yanzun nan ba yave kai hajiyata ya zan barta bayan hakkin ci da ita yana kaina to ba gashi ka wadata tada abinci ba ta juyo ana zabga ma fatima hararra tace ke wato baki san kizo ki gaisheni ba ko? " turo baki fatima tayi tace inzo ki cika min kunne da masifarki la'ila la illallahu tunkaro fatiman tayi ita ko ta fece da gudu ta shiga daki tana dariya baba karami ma dariya abin ya bashi yana jinjina rigimarnfatima da kyar ya lallashi hajiyar ta koma gefenta shi kuma ya tunkari dakin fatiman.

SAWWAMA QAWWAMAA
 
RIBAR BIYAYYA by sawwama page 4,5,6,7,8,9,10

Load Comments

Subscribe Our Newsletter

Notifications

Disqus Logo