Thursday, February 13, 2020

BURIN HAFEEZ complet novel, ebook

BURIN HAFEEZ complet novel, ebookBURIN HAFEEZ
littafin Aisha


KADAN DAGA CIKIN LITTAFIN

Episode 1⃣


Tasss!! Kakeji ya wanketa da kyakyawan mari, cikin hargagi da tsananin masifa yanuna ta da d'an yatsa yace "ke dabbar inace? Kina gani lokacin da nake 'ko'karin kauce miki amma saboda tsabar dabbanci da 'kauyanci irin naki shine kike 'ko'karin shigemin, salon naje nabugeki kijawomin zuwa asibiti"

A gigice ta ri'ke 'kuncinta wanda yakemata tsananin rad'ad'i da azaban ciwo, batareda ta kallesa ba, cikin sassanyar muryanta tace "kayi ha'kuri, nima ba a son raina hakan yafaru ba, kaina ke tsananin min ciwo, hajijiya ce ke d'awaniya dani bansan lkcn da na tunkari motanka ba, kayi ha'kuri"

Tana fad'in haka tudu'ka tad'auki bokatin awaranta wanda yazube a 'kasa, ta ratsa ta gefensa tawuce, sakin baki yayi yana binta da kallo, cikin zafin rai yace "ke!!!! Zonan"

Batare da ta kalli inda yake ba tajuyo jiki asanyaye, qarasowa tayi gamida duqe kai cikin sassanyar muryanta tace gani, wani irin iska mai d'aci Hafeez yafurzar gamida xaro manya-manyan idanunsa fuska a hargitse  yace ke waye ubanki agareni nan? Da har adalilina xaki xubar da kayan tallanki amma kikasa budan baki kice nabiyaki, damekike taqama stupid grl?
Wasu irin xafafan hawaye ne ke kwaranya akan kod'ad'iyar fuskarta, cikin nuna rashin jindadin kalamansa tace" kai kuwa bawan Allah kai wanne irin mutun ne? Naga tunfarko nabaka hakuri sannan kayan sana'ata da suka xube bana buk'atar kabiyani" meka dauki kanka?

Toh bari kaji niba irin yan'matan nan bane masu son cece kuce akan titi ba, sannan kana mgnr cewa waye ubana' umhm ubana shi ba kowa bane, kmr yadda kasani baxai iyaja da mnya kmr Ku ba. Tana fadin haka ta gyara jemammen silifas dinta wnda yake qoqarin fita a qafarta tacusa qafarta ciki tafara tafiya cike da sanyin jiki' cikin xuciyarta kuwa wani irin baqinciki da qunci gamida d'umbin damuwa ke d'awainiya da ita.

Abangaran Hafeex kuwa ko k'wak'waran motsi yakasayi sbd tsananin mamaki da ya kamashi kasancewar tunda yake ganin yan mata kala-kala masu aji da marasa ajin babu wacce ya tab'a ciwa mutunci ta maida mishi da marta sai wannan jamammiyar talakar yarinyar" cikin tsananin fushi Hafeez ya fara takawa da nufin isa gurin wannan yarinyar, ae kuwa da sauri wata kyakyawar matashiyar yarinya tafito acikin motar da sauri gamida riqo hannunsa tace "plss Yaya Hafeex don't do dat 4god sake, tundaxu ina kallonku fa kasanar da ita laifinta Kuma wannan baiwar Allahn ta amsa laifinta har tabaka hkri" plss yaya kaxo mutafi gda ni ynwa nakeji gabadaya am vry tied, 
Fuskan nan ta Hafeez kuwa kokad'an  babu fara'a yace look Balkisu pls ki k'yaleni inje inkoyama yarinyan nan tarbiyya,sbd na lura kokad'an bata da manners, cike da shagwab'a Balkisu tafara bubbuga qafafunta kmr xatayi kuka "plsss yaya nidai ka kyaleta kaxo mutafi gda," Hafeez yasake waiwayan wannan yarinya amma tuni tab'acewa ganinsa..wata uwar kwafa yayi gamida Jan tsaki ba haka yaso ba dan haka bashida wani xab'i dayawuce yashiga mota sutafi.cikin qasan xuciyarsa kuwa wani irin haushine yacikasa sbd gabadaya haushin knsa ma yakeji da bai qara marinta ba.

Al'asfar Restaurant yawuce da ita kai tsaye, sbd Hafeez Sam bai qaunar ganin Balkisu na complain akan yunwa, abinci kala-kala masu kyau da tsada yasa aka kawo mata. Taci sosai"shikuwa Hafeez sbd b'acin rai koh abinci yakasaci, babu yadda Balkisu batayi akan Yayan nata yaci abinci ba amma Sam yaqi., hakanan Balkisu tadaure itama tadanci abincin ba wai don ranta yaso ba..

Jiki a sa6ule suka nufi gda, shigarsu keda wuya Hafeez yanufi sashensa cike da 6acin rai' abangaran balkisu kuwa nadama ne gamida Danasani fal acikin xuciyarta.domin kuwa ita kanta tasancewa itace silar wannan fushin nasa 
Sbd tahanashi aikata abinda take ganin shine dai-dai,

Acikin wannan dare kuwa daga balkisu har Hafeez babu Wanda yaruntsa, sbd kowa da tunanin da yakeyi cikin zuciyarsa. Abangaran Balkisu kuwa talashi takobi gamida alqawarin sai tanemo wannan yarinyar a dukk indatake, sbd tabama yayanta damar cikar Burinsa.

Da wannan tunanin nannauyan bacci yyi awon gaba da Balkisu........ 

DOMIN KARANTA CIKAKKEN LITTAFIN SAI KI DOWNLOAD NASHI A NAN KASA

DOWNLOAD THE NOVEL NOW

DOWNLOAD FROM OKADABOOKS AT 150#

Saturday, February 1, 2020

BARRISTER ASSAD complet

BARRISTER ASSAD complet

BARRISTER ASSAD

COMPLET EBOOK


KADAN DAGA CIKI

Alhaji Muhammad Ali babban Dr ne mutum ne d'an boko sosai asalinsa buzu ne amma 'a Nigeria ya tashi Allah ya basa ilimi sosai bayan kasancewar sa Dr kuma Professor ne yanzu haka yana da asibitin kansa, matar sa d'aya 'ya'yanta uku Ibrahim da Nabila sai kuma auta Sadiya amma suna kiranta Jalila kasancewar sunan mahaifiyarta ne da ita, Ibrahim da Sadiya sunyi karatu mai zurfin gaske gashi Allah ya basu baiwar k'wak'walwa kullum su suke d'aukan over roll students, Ibrahim yanzu haka ya kammala PHD d'insa yayi aure 'a chan Uk kasancewar 'a chan yayi karatunsa koda ya kammala karatunsa da first class upper ya fita shine best student of the year wannan dalilin ne yasa suka d'aukesa aiki!


Nabila kuma sai da ta kammala master's nata tayi aure lokacin tana 20years tayi aure ita ma Allah ya bata k'wak'walwa ita ma tana lecturing 'a ABU dan 'a Zaria tayi aure...ita ne the most youngest Lecturer 'a ABU English 'a bakinta kaman me dan Slang take yi......tun tana k'arama mahaifinta da mahaifiyarta basu yi wa 'ya'yansu Hausa sai dai English wannan dalilin ne yasa in suna speaking kaman 'ya'yan turawa, shima mijin nata mugun d'an boko ne shine Chancellor na school d'in
Jalila 'yar auta kam ba'a magana dan ita Allah bai had'a jininta da karatu ba kullum na 6 ko 7 take zuwa yayunta kam basu tab'a wuce first position ba, Jalila bata ji ko kad'an kullum sai an kawo k'ararta gida...Jalila sam bata ji gashi bata da mutunci ko kad'an ga rashin ji, ga rashin kunya, surutu, fitsara, fitina duk ita d'aya dan indai tana wuri sai ansan tana wuri, gashi tana da son hayaniya in tana abu wane 'yar daba!
Duk friend's nata maza ne shiyasa ita ma behaviour nata na maza ne


Duk zafin iyayenta sun rasa ya zasu yi da ita...dan mahaifinta yana da zafi sosai amma tunda Allah ya basa Jalila yayi sanyi gashi Allah ya d'ora masu sonta ta kad'an ba, amma basu nuna mata irin sosai d'innan saboda irin halin yaran zamani.....tana k'aunar iyayenta sosai ba kad'an ba wannan dalilin nema yasa take gudun b'acin ransu dan in ransu ya b'aci hankalinta mugun tashi yake yi koda ba ita ta b'ata masu rai ba in taga ransu ya b'aci sai ta zauna tayi ta yin kuka
yanzu she's 16years this year zata gama secondary school, amma sai ka ranste she's 14 dan wautanta is worst
Zaune take hannunta rik'e da littafi amma ba karatu take yi ba hankalinta na kan Tv sai taji motsi tayi pretending as if she's reading dan ace tana karatun exams,
Mami ne ta shigo palon tare da Daddy
"Baby girl karatu ake yi?"
Fake smile tayi tana jin dad'i tace
"Yes Dad"
Girgiza kai Mami tayi tace
"Am certain she's not reading, she's just ptetending"
Tuni ta fara hawaye
"Mami am reading fa"
Murmushi tayi tace
"Yawwa good girl reaction naki ya nuna kina karatu da gaske good girl"
Dafa kanta Daddy yayi yace 
"I promise in kika yi k'ok'ari in your Exams i'll buy you latest iPhone da makeup kit"
Tsalle tayi ta fara yi masa godiya


Tun daga ranar Jalila ta zama serious kullum ka ganta karatu takeyi tsakaninta da Allah dama already wayanta ya lalace babu chating, kallo ma bari tayi...dan school d'insu ba'a bayar da Exco na Waec and Neco
'A haka har suka gama Exams Jalila ta dan nustu tana karatu koda Result ya fito Jalila tayi k'ok'ari sosai daga A sai B..A sunma fi yawa dan ita ma tana da k'ok'ari kawai karatun ne bata so...the next day Daddy ya cika mata alk'awari ya saya mata Makeup kit had'e da X d'inta ranar kasa bacci tayi dan farin ciki
Tun daga lokacin labari ya chanja Jalila ta chanja friends sai masu x ne friends nata, rashin ji ko k'aruwa yayi Daddy ya kai ta training na computer kafin 'a fara bayar da admission, Jalila kam da driver ya ijiye ta take k'arawa gaba yawo dan wannan new friends d'in nata fitinannu ne, gasu da shegen yawo kullum suna kan titi posting kam ba'a magana dan IG and Snap sun san da zaman Jalila, Modelling ma ta fara duk wasu photographers sun san da zaman ta...makeup artist duka dai hotunan ta sun gama zaga duniya
Rashin ji kam ya k'aru da kula samari dan duk wani matashin saurayi yasan da zamanta, samarinta basu irguwa....duk abinnan da take yi Daddy da Mami suna sane kawai sunyi mata shiru ne...may be they are up to something!


Zaune take 'a kitchen ta mik'e k'afa tana yanka Alayyahu duk ta b'ata wurin wane wata mara hankali Mami ne ta shigo tsoki tayi had'e da galla mata harara tace
"Wai Jalila yaushe zaki yi hankali? Yanzu yanka alayyahun shine kika b'ata duka kitchen d'in?"
K'asa tayi da kanta tana murmushi, tsoki tayi tace
"Aurar dake zanyi na huta na wannan iskancin naki"
Turo baki tayi tace
"Ni aure 'yar k'arama dani Allah ya kiyaye...Anty Nabila ai sai da tayi karatu aka mata aure"
Rankwashinta Mami tayi tace
"To fitsararriya ai sai ki zage ni"
"Kwarai da gaske aurar dake zamuyi ai kin sa ja'ira kawai" Taji muryar Baabaa mai aikin su tana shigowa
Murgud'a baki tayi tace
"Ai sai ki aurar d'in"
Rankwashinta Mami tayi tace
"Ohhh fitsararriya da Baabaa zaki yi?"
Murmushi Baabaa tayi dan sun saba yi da Jalila kullum sai sunyi fad'a kuma still suna shiri dan bakin Jalila bai yin shiru da sunyi fad'a zata cigaba da bama Baabaa labari in tayi banza da ita ko tana amsa mata Emm...sai ta bata hak'uri dan ta iya bayar da hak'uri ba kad'an ba... 

DON JIN CIGABAN LITTAFIN SAI KU DOWNLOAD NASHI A NAN KASAMonday, January 27, 2020

JUYA complet

JUYA complet

JUYA

Littafin Feenat jafar
Complete


KADAN DAGA CIKI

.
1_A gaban mudubi take tana k’yali,ta shafa nan,ta shafa chan,ta mudubin kuma tana d’an k’allon ta cikin shi tana murmushi, ganin yadda mutuminta ya zuba mata ido ta ciki.
Juyowa tayi,yai d’ai-d’ai akan gado yana k’allonta, d’uk rashin k’yau na abu,toh mud’in kana muradin shi mai k’yau ne a wajen ka. Babban mamakin shi yadda ya kasa ganin munin Matarshi a kullum, yakan shafe “seconds” dan gano ta inda “Prettyn”shi ta gaza, kai ya girgiza, dan shi baiga makusa ajikinta ba ko kad’an.
D’uk a kullum dangin shi suna mishi gorin d’uk k’yawawan garin nan,amma ya rasa wacce zai jaju6o sai Fulera,ga ta “JUYA”,ta bare suce ko dan haihuwa taci darajar so,,d’uk ta tare gaba,ta tare baya, ta hanashi ganin d’uk wani makusa tata a gare shi,balle yai tunanin gazawarta na zama “JUYA”.
Asalima shi in d’ai zai tozali da Fureran shi”Pretty” toh yakan manta komai.
“Pillow” ya sake jawo wa,lokacin da ya g’yara k’wanciya yana cigaba da k’allonta, d’ai- d’ai da dak’ika d’aya baya fatan yaga “Pretty” ta barshi,yana matukar k’aunar ganinta kusa dashi. Bai aune ba ya ji ta hure mishi ido da bak’inta tana murmushin nan wanda ke sashi murmushi ko da bai shirya ba,, kamshin “lestrine” ya buge shi, had’i da kamshin alawarta ta kullum,”splash”. Take ya sau ajiyar zuciya, kan ya k’allota.
Hakika yana kara godiya ga Allah mad’aukakin sarki da ya bashi “Pretty” a matsayin “Matarshi” kuma “Sanyi ga Idanunshi”. Tabbas yana daga cikin maza masu t’sant’sar sa’a a rayuwa na samun “mace ta gari”,wacce ganinta kad’ai, ya isa wanke maka bak’in cikin rayuwa,har yai hamdala da mahaliccin shi,dan ya mishi baiwa,irin wacce ba Kowanne namiji ke da ita ba, a ganin shi,dan ya hanashi “D’a” bazai zamu ya masa butulci ba.
Murmushi ya sakar mata,kamar kullum ya fara yaba mata wankanta. “Kinyi k’yau sosai pretty, a kullum ranakun duniya kamar ana dad’a kawata min ke ne,kamar ki zauna nai ta k’allon ki kawai.
“Ko zaki fasa zuwa sunan?
Murmushin jin dad’i tai,gashi d’ai kullum irin kirarin nan tana shan su,amma baya hana taji dad’in jinsu.
Zama tai, tare da ruko hannunshi ta kai baki tai”kissing” take k’wa ya sauke ajiyar zuciya,tare da d’aura d’ayan hannunshi kan nata..
Tsaf ta riga da ta gama samo abinta cikin ruwan sanyi, ta riga da ta gama sanin d’uk wani “week points” nashi akanta, mai lafazi mai k’yau ce ita da sanyin murya, takan ko’k’arin tauna zance,sannan ta ya6a mishi”gold” da “lu’u-lu’u kan ta bashi.
Cikin salon ta da wata irin murya ta fara magana tana lumlumshe mishi ido da d’an lallashi. Ji yake mar rad’a take mishi a kullum.
“Kar kaji kom “Nawan” ni taka ce ai,k’walliyar ma taka ce, zan rintse ta ga ganin kowa,sai d’ai in mata y’an uwa na, badan sanin mahimmancin sunan nan a gare ni ba,da zan ta zama,kai ta k’allo na,har sai kace na ishe ka.. Ta karasa tana fari da idonta, take k’wa ya sau ajiyar zuciya.
Unguwa ko bai niyar barin prettyn shi ba,da kalam kawai zata sa ya firta “Toh”.
Kai ya girgiza kan ya tashi ya zira rigarshi.
Ita kuma ta sa hijab da Nikaf dan rufe k’walliyar.
Tafe suke a mota,suna ta faman firar duniya cikin nishadi,har ya faka a kofar gidan sunan,wanda matar K’aninshi take gare shi.
Hannunshi na cikin nata,tambayarta yake sai yaushe zai zo d’aukan ta? Ganan wasu na shiga,wasu kuma na fita a gidan sunan,sai d’ai in sun fito,maimakon su tafi,sai suja su tsaya k’allon su prettyn.
Tana shiga ta tsaya ta cire nikaf d’in, kan tai bangaren mai jego.
Da sallama ta shiga d’akin fuska sake, fal cike da jama’a, kowa ya zuba mata ido, ta samu gefen gad’on ta d’an dosa na,tana kula da hararar da wasu ke sakar mata,”ina yinin ku.. Fuska mai jegon ta yamitsa,kan tace”sai yanzu? Dad’i Miji.. Murmushi tai,dan tasan da ta tofa yanzu za’a fad’a mata magana. Cigaba tai, “shidai cin tuwon kishiya ramako ne,ehee. Kai ta k’ada, lalle mutum.
K’anwar mijin tace ta amshe,”ba Kowanne tuwan bane na ramako..kar ma kisa a ka,a yadda tai shirim d’in nan ne zaki sa rai? Baki ta ta6e,kan tace suna ga wata wai “JUYA” tashi tai “parlour” tana hararar prettyn,wacce ke mata murmushi...

DON CIGABA DA KARANTA LITTAFIN SAI KU DOWNLOAD NASHI ANAN KASA


Thursday, January 23, 2020

AUREN SIRRI 1 to end

AUREN SIRRI 1 to end


AUREN SIRRI

COMPLET NOVEL 
NA AISHA A BAGUDO


KADAN DAGA CIKILekki  Unguwace  mai dauke da karancin mutane da suke rayuwa acikinta   ,a silent place, saboda bata cika   hayaniya mutane ba  , dauke da tarin sanyin ni'ima mai dadi  sakamakon kusancinsu da ruwan teku" unguwace da tattara kan manya ma'aikata da kusoshin gwanati, hade da manyan masu kudi ,ga tarin  yan yahoo boy'z  domin mafi yawancisu   sunfi sha'awar  zama acikinta. rayuwar mutane  unguwar abin sha'awa  bbu ruwan wani da wani  domin suna rayuwasu ne tamkar a kasar waje   .


PLASNUW ROWS FAMILY ESTATE 

Estate ne mai dauke da tarin dangi acikinta , hadin kai tattare da zaman lfy,  Sam bbu hayaniya acikin wannan family kowa kagani cikin nishadi da farinciki zaka gansa ,ga tsantsar fahimtar juna dake tsakanin wannan family. kwakkywan family ne masu matukar kaunar junansu .


Let alh Muhammed bello khaliyal ,haifafen garin Lagos ne ,Amman asalinsa fulanin khaliyal ne dake jahar kebbi. sananne  mai kudi ne yayi tashe tun alokacin da duniya ke kwance. sannan kuma take zaman lfy, marigayi Muhammed bello  soldier ne daya taka rawar Gani a kasar nan .
 ya rike mukamai da dama a wancan lokacin. ya rasu yabar tarin dukiya da da ya'ya da jikoki  bila adade.
    gabadaya family Muhammed bello bbu talaka aciki  domin sun gaji dukiya mai tarin yawa daga mahaifinsu  .

 kafin rasuwarsa    dake shine babba a dakinsu kuma Allah yabashi tarin dukiya da en'uwan , dan ganin ya inganta rayuwar kannensa kafin daga baya ya Gina wannan katanfarin estate din  mai mazan kanta.
 ya tattara  kan yan'uwasa suna zaune a ciki ,yana da mata hudu  hjy  shema'u  wacce aka musu aure tun saurayi da budurwa tana da ya'ya  goma   Sha biyu, mata takwas maza hudu  sai hjy  hauwa mai dauke da ya'ya goma maza biyar mata biyar ,sai hajiya rabi mai ya'ya takwas maza biyar mata uku   sai hajiya Fatima wacce suke kira da hjy  shuwa  itama tana   da yaya takwas mata bakwai namiji daya .
 bbu abinda bbu acikin wannan estate din kama daga makarantar islamiyya wajen wasa buga kwallo wajajen exercise wajen swimming pool library Sannan ga wani katanfarin Holl dake gefe wanda aka shiryashi da kayan kyale kyale zagaye da kujerun zama . an ginashine  saboda  taron sada zumunci , wanda zasu dinga yi a duk karshen wata  .

 haka suka taso har zuwa girmansu cike da son junansu .
 anan cikin  dangi mazan suka zabi matan suma  matan suka zaba akayi  bikinsu anan cikin estate din suka zauna  tare da iyalinsu  har zuwa  sanda tsufa yacima marigayi Muhammed bello yayi retire.
 yayinda ya'yansa da ya'yan en uwa suka cigaba da kula da estate din .
  a lokacin  aliyu  da  habib ne kadai suka rage da basuyi aure ba saboda  karatu . 

Byn rasuwar marigayi bello ne aka raba gado aliyu  ya dukufa  gurin juya dukiyarsa ,ba abinda  yasaka a gaba sai neman kudi wanda acikin kankani lokaci ya gawurta yayi fice yayi suna a duniya,  yayiwa sauran yan'uwansa zarra  aliyu ya mallaki tarin dukiya da shi kansa bai san iyakarta ba. hade da tarin compenis  a Lagos da kudancin Nigeria yana da gidajen saida man petir Bila adadi shine mallakin aliyu airlines yana da hannu jari da dama a compenis na kasashen duniya yana da  gidaje a abuja da sauran garuruwa .
tsananin neman kudinsa ne yasa  bai ajiye iyali da wuri ba ,burinsa bai wuce  ya auri mace mai matukar kyau da tarin illimi ba .

Garin neman kudinsa ne ya hadu da fadila  a india tun daga lokacin da aliyu ya daura  idanunshi akanta "ya dauki son duniya ya daura mata kasancewarta kyakkywa gaske ga tarin illimi . fadila itace Diya ta biyu a gurin iyayenta su uku ne , ahmed  ne babba sai ita sai farida ,  kin amincewa iyayenta sukayi da auren shi a cewarsu bako ne sannan kuma bakin fata. sai da aka kai ruwa rana dasu sannan suka amince  da auren .
 koda yazo daita Nigeria ma bata wani sha wuyan zama cikin family dinsa ba .
kasancewarta mace mai tsananin  son jama'a da son yara cikin lokaci kadan tashaku da sulaiman da  mahamud ya'ya ne ga yayyen aliyu sun shaku matuka da yaran ta daukesu tamkar ya'yan data haifa  acikinta .
suma  kuma suna maseefar kaunarta dan haka suke   kiranta da ummi ,duk abinda suke so itace take musu bata ragesu da komai ba saboda bata da rowa  hakan ne yasa ta sake janyo mata soyayya ta daban a gurin iyayensu.

 shekarata biyar da aure mutuwar mahaifiyar ta risketa ,zuwan datayi indiya ne dazata dawo tazo da kanwarta fadila  ta hada dasu Mahmoud tacigaba da rikonsu .
 sai da fadila ta dauki sama da  shekara takwas  da aure  sannan tasamu cikin murna a wajen wannan family bai faduwa .
    cikinta na da wata tara cif ta haifi NASURUDEEN  daga ita har aliyu suna matukar son DEENI tamkar numfashinsu DEENI yataso cikin gata da kulawar iyayensa, da dangi gabadaya suna nuna masa tsansar  gata da soyayya fiyye da tunanin mai karatu .
shiyasa yataso a shagwabe a sangartacce saboda kaf estate din  kowa yasan da zaman DEENI babbar matsalar da suka fara fuskanta da deeni  , shine rashin magana da bai yi ,da farko fadila  ta dauka ko kurma ne sai daga baya tagane tsabar miskilanci ne kawai yayi masa yawa .
duk tarin ya'yan dake cikin wannan estate din DEENI yafita dabam acikinsu,   bashida aboki  ,.
 gabadaya baya yarda da kowa  koda yaushe  yana tare da umminsa ko farida ko su  Mahmoud tun tasowarsa yake da burin son zama soldier yayinda ummi take bashi goyon baya wajen kiransa soja .
Domin  wani lokacin zai je yatasa hotonta marigayi kakansa dake manne a falonsu gaba yayi ta kallo yana shafa fuskar tsohon yana murmushin ,Sam shi  bashi da fara'a ballanantana sakin fuska   koda yaushe fuska nan tashi a hade take tamkar hadari , .DEENI Nada shekara takwas byn yakare primary school aka sai mishi form din  shiga makarantar sojoji ba'awani samu wata matsala ba yasamu  sakamakon matsayin mahaifinsa da kakansa. sabanin wayanda  basu da gata.
 domin a wanan lokacin idan dai kai bawani  bane  ko dan wani  ba  ko bakada  hanya a military school  ,sunanka sorry.
Domin kuwa  kana ji kana Gani  military school zai gareka shiga  .

    byn wani lokacin farida ta samu miji anan cikin estate din  wanda shima    yakasance "Da"ne ga marigayi  Muhammad bello wato  habibu ubansu daya da aliyu mahaifin ga DEENI   .
duk da fadila ta nuna rashin amincewarta matuka , da nuna wa er'uwartata illar aurenta da Habib   Amman sai taga yarinya ta nuna tana so abunta  ,dan haka ta kyaleta kuma da kunya dai ta fito fili tace batason jinin aliyu ,wanda itama kanta tasan hakan ba mai yiwu bane . itama ba wai shi din ne bataso ba ,halinsa ta tsana , 
Amman shi babban  ma'aikace  gwanati ne,   director of land  and housing & same   na Lagos state gabadaya. yana da mata biyu da yaya bakwai farida ce ta uku . 
Ko alokaci daya auri   farida   takasance mace ce mai tsananin hakuri .
duk da mijin nata Vai kasance mutun  mai adalci ga iyalansa ba. Amman bata taba kawo kararshi ga ummi ba domin tasan halin ummi Sam bata son raini .

Shekarar da aka yiwa sulaiman da mahamud aure shekarace Allah yayiwa mijin ummi rasuwa wato alh aliyu Muhammad bello sunji matuwar farar daya  , mutuwar tayi matukar gigita ummi dan byn ya dawo  daga sallah asuba ne yayi irin kishingide nan yana lazimi  koda ummi taji shiru shiru bai sake fitowa ba Sannan bai nemeta ba  kmr yadda ya saba , wanda aldarsa ce  da zarar gari yayi sha ...yake fitowa ko yakirata a waya    Amman taji shr .
 tashiga dakin nasa  ta tarar dashi kishingide da carbi a hannunsa .
 da fari ta dauka ko bacci yakeyi sai tayi nufin ta tasheshi yakoma kan gado.
  Ammai sai taga alamun rashin motse atare dashi takai hannuta wajen hancinsa da karjinsa a lokacin daya taji baya numfashi.
   take ta zube anan ta sume.
 har a kashare zaman makoki ummi  batasan a wani hali take ba ,dan   bata  cikin haiyacinta' koda ta farfado ma sai da akayi ta hadawa da addu'a Sannan aka samu kanta ta dawo daidai , dan mutuwar ta girgiza har ta kusan zarar daita  .

Byn wani lokacin  su sulaiman suka cigaba da tallafawa ummi da DEENI a lokacin farida na dauke da tsohon ciki  duk da itama ta dan jima bata haihuwa ba, kuma har lokacin ummi bata san er'uwarta tana cikin matsala ba ,sai byn data haihu" lokacin ne ummi taga komai bbu alhalin ga tarin dukiya kmr zai kashe habibu , gashi yasake kara wani sabon  auren matansa sun cike hudu cif .
ummi tayi kuka kmr may  gashi tana cikin danginsu da suke tamkar tsiya madauri daya.
 ba daman tace zata dauki wani mataki akan  haka  .
dan tasan yadda kansu yake a hade .
    dan haka taci kukanta  takoshi ita da er uwarta ahankali take furta kalmar shiyasa tun farko naki amincewa da auren nan naki da habibu ,ba dan komai ba sai dan irin haka  Amman kika nace ,ga  irin abinda nake gudar miki kennan Amman kika kiji , sai kuma ta tsagaita da kukanta ahankali  tace  ba yadda zamuyi da ikon Allah ,sannan ga rabo a tsakani.
 Amman duk da haka sai da ummi tayi masa tatas saboda daman ita bawani sakar masa fuska take ba kuma  yana shakkata.
 kullum ummi acan take wuni har ranar suna    yarinya tace sunan mahaifiyarsu ummi wato muzeenat ,  shima habibu yayi hakan ne saboda ya wanke kansa a wajen ummi,kuma yayi nasara domin  hakan da yayi  yasa ummi taji dadi Sosai aranta har ta dan rage jin zafinsa .
 sannan bakaramin kudi ummi takashewa bby ba. haka ma   ranar suna ummi Tayi rawar Gani sosai .
byn anyi suna ne ummi  tasamu habibu akan dan Allah  ya dinga kula da farida dan ita kadai gareta bata da kowa duk fadin Nigeria sai ita,  idan ma bazai damu ba,  zata bashi Rabin dukiyarta yakara akan nashi  da duk wani  abinda yake so, ita dai burinta kawai ya kular mata da er,uwa ,yayi murmushi kawai hade da ce mata yaji  .

Byn wani lokacin farida ta kuma samun wani ciki wanda tun yana karami take fama da laulayi tun lokacin ummi tadawo da zeenat wajenta ,
a kwana a tashi bbu wuya a gurin Allah har cikin farida ya isa haihuwa gurin haihuwar ne taji jiki sosai .
koda     ta haifi yaron ma  bbu rai sannan itama tace ga garinku .
mutuwar ta shigi habibu matuka yayi kuka tamkar ransa zai fita ,dan shi kansa yasan yayi babbar rashin  da ba zai taba maida irinsa ba.
  yayi rashin mata  mai tsananin kirki da hakuri da sanin darajar miji . Allah sarki ummi   kusan har  tafi habibu jin mutuwar tilon er'uwarta ta ,.
a  wannan Lokacin ne  rikon zeenat ya dawo dindindin  gurin ummi ta dauki soyayyar duniya ta daurawa zeenat tana mugun ji da Yarinyar   tamkar ranta kwata kwata bata son abinda zai rabata da zeenat Sannan kuma   tana debe mata kewar er'uwarta .
lokacin shi  DEENI   na ss1  a NMS, Nigeria military school dake zariya.
   yayinda DEENI Sam ba halinsu daya da ummi ba koda yaushe kagansa fuskar nan tasa  a daure a cunkushi  bbu wani fara'a ga shegen miskilanci tsiya  sai dai mugun kyakkyawa ne na karshe . ajin farko, wato first class ,gashi  da  maseefar  iya sa kaya kallo daya zaka masa ya gigitaka kaji yashiga   ranka farar daya saboda tsabar kyawunsa sai shegen shiga ran mutane domin kusan yan'mata cikin  estate din suna maseefar son sa yayinda yake  girma kyawunsa na sake bayyana hade da miskilancinsa     .

Tunda zeenat ta dawo gidan magana bata taba hadasu ba ko gaisheshi Tayi baya amsawa in dai bayaga idanun ummi ba yana da matsanancin tsafta wanda kusan a wajen ummi yagada .
Cikin haka ya kammala karatunsa na secondary school ya wuce NDA burinsa kennan nason zama cikakken soja itama  ummi kuwa  nasake karfafamasa gwiwa da bashi goyon baya   yana karantar science ne ,wato likitan soja .
bansan yadda zan kwatanta muka  halinsa ba Amman yakasance mutun ne shi mai bambanci ra,ayi.
 byn yakare karatunsa ya fito da mukami second lieutenant star biyu  kennan   .

Zaune zeenat take a falo tana kallon wani serisfilm  a zeeword my let home Tayi zurfi cikin kallon film din gabadaya attention dinta naga kallon ita kadai ce ummi tashiga cikin estate din yin barka taji karar Bell wanda shine kusan karo na hudu da taji ana dannawa. cikin jin haushi ta mike dan bata son abinda zai dagata daga kallon datakeyi , tana bude door din bata tsaya ganin kowaye ba ta juya abinta takoma mazauninta  sallama taji  hade da shigowa ta dago kanta  kennan   da niyar amsa sallama sai taga mutun tsaye kikam  sanye da sabon  kayansu na  sojoji gabadaya zeenat ta gigice hade da rikicewa tsabar tsoro dan ita Allah yayita  da maseefar jin  tsoron soja   take cikinta ya dauki kugi Amman still  idanunta  na kansa ta tsaresa da  kallo .
  in ina tasoma yi wa..wa.. waalai....ya dakatar daita da hannushi, yana zabga mata wata uwar  harara muryasa a kwasashe yace yau ne kika fara ganina  da har zaki wani  tsareni da idanu Kona canza miki ne ?da sauri tasoma girgiza masa kai. Kai tsaye dakin ummi ya nufa tunda bai ganta a parlour ba yasan tana dakinta  tana kallonsa ta kasa dauke idanunta daga garesa har sanda ya dawo fuskar nan tasa a hade yace ke.....dan iskanci kina kallon mutune bazaki iya cewa  ummi bata nan ba   kin wani tsare mutun da idanuwa tamkar na maciji ,dayake bawani manyan idanu gareta , da sauri bakinta na rawa tace dan Allah kayi hakuri mantawa nayi  ko kallonta bai sake yi  ba yaja tsarki yayi hanyar dakinsa  ta tabe baki hade dacewa   jarababbe kawai ai  yadawo kennan, itama taja tsaki ta juya tacigaba da kallonta ..


DON KARANTA CIGAGABAN LITTAFIN SAI KU DAUKO SHI A NAN KASA


Tuesday, December 31, 2019

Thursday, December 19, 2019

Monday, December 16, 2019

Sunday, December 15, 2019

Sunday, December 8, 2019

GANTALALLIYA complet

GANTALALLIYA complet


GANTALALLIYA
Na Deenluv
Complet

Assalam jama'a bayan shiru da mukai na kwanki biyu gashi mun taho maku da wani littafi mai matukar dadi gamida nishadantarwa na marubuciya Deenluv

About book
Wata zukek'iyar bakar mota kirar benz E350 na hango ta karyo kwana, wani dankareren gida ta tsaya, yana matsa horn mai gadi yataho da gudu ya bude gate, sannu da zuwa yakeyimas bai tsaya ya sauraresa ba ya wuce inda ake parking motoci.....


Maigadin yana rufe kofar yabi bayan motar da sauri, kan ya isa har mutumin dake cikin motar ya fito, gaishesa yayi tare da yimasa sannu da zuwa.....

"Yawwa sannu sabo, madam tana ciki ne ko tafita" yake tambayar mai gadin, daidai lokacin dayake bude kofar bayan motar yana dauko jakar sa.

"Ai ranka shi dade baka dade da fita ba wata mata tazo naga sun fita tare, kuma har yanzu basu dawo......." daga mishi hannu yayi rai abace yace "shikenan nagode zaka iya tafiya" 


Yana shiga cikin gidan, tundaga bakin kofa yafara karo da shirgi kalakala, tsaki yayi ya wuce dakinsa, wanda yasameshi a yanda ya  fita ya barshi, wani takaici ne ya rufeshi, kamar yayi kuka, ga yunwa daya kwaso.

Da kansa ya kyara dakin sannan ya fito kitchen domin yasamu abinda zaisa a bakinsa. Yana shiga idonsa ya kai kan gas cooker din, tayi dak'al dak'al, dagani tunda aka siyeta bata taba ganin ruwa ba, haka ya daure ya dauko wata yar karamar tukunya, itama seda yadaurayeta sannan ya dora ruwa, wanda baima san abinda zae dafa ba.


Fridge din ajiye kayan miya ya bude don yaga ko zae samu ragowar miya sai ya dafa farar shinkafa, yana budewa ya rufe da sauri, dan tsabar wani wari daya doshi hancinsa, nan take yaji amai ya taho mai, da gudu ya kashe wutar gas din yayi waje da sauri....


Tun a kofar kitchen din yafara sakin aman, ga wani jiri dayake dibarshi, haka yayi yagama, da kyar ya gyara wajen yayi dakinsa, toilet ya fada ya sakarwa kansa shower, sannan yasamu ya dan ji dadi.

Yana fitowa ya suri key din mota yayi waje, ba motar daya dawo da ita ya hauba yanzu, wata jar mota ya dauko an lullubeta da bakin tinted, yana fita bai tsaya a ko  ina ba sai a chicken castle....

Anan yasamu yaci sakwara da miyar agushi, ci yake kawai amma zuciyarsa babu dadi. Yana gamawa ya koma gida, misalin karfe 6 na yamma, amma bata dawo gidan ba, sai yayi tunanin ya kirata a waya sai kuma ya fasa.

Kwance yake akan gadonsa kamar mai bacci, amma kuma ba baccin yakeyiba illa tunane tunane da suka shige mishi kai.

Ba ita tadawo gidan ba sai goma saura yan muntina.... 

Buzubuzu ta shigo gidan, daganin tafiyarta kasan babu nutsuwa atare da ita, gashi sai taunar chew gum take kai kace ba mace ba, bama wannan ba, shigar da tayi ma kadai ya isa kasan wacece *BINTU MATAR SADIQ.*

Dakinta ta wuce tayi wurgi da jakar hannunta tana "washhh!!! Nagaji wallahi" kayan jikinta ta cire ta wurgarsu a tsakiyar dakin,ta  dauko wata doguwar rigar bacci,wacce inbanda tsami babu abinda takeyi, amma haka ta tafka abinta ko ajikinta...

Kan hargitsetsen gadonta ta hau ta kwanta abinta, wayarta ta dauko takira wata kawarta, saidai bata dauka ba, haka ta gaji ta ajiye ta ja bargo ta shige....

Shikuma tunda yaji shigowarta yakasa daurewa seda ya tashi ya biyota har dakin nata. A fusace ya shiga kamar wanda zai daketa sai dai yana zuwa yaji gabansa yayi wani irin mugun faduwa,a sanyaye ya karasa gabanta..


"Haba bintu! Ina kika tafi kika kai dare haka batare da kin sanar dani ba" shiru tayi kamar ba da ita yake ba, seda yasake magana ta dago a fusace "haba malam kafa takura min nidai wallahi, nadawo ma ko sannu da zuwa baka min ba sai tambayar daga ina nake, to unguwa naje koda magana ne? Girgiza mata kai kawai yayi kafin yace "Allah ya baki hakuri" tsaki taja "aikin banza kawai, nikatashi kafitar min adaki bacci nakeji" bata jira cewarsa ba taja bargon ta koma.

Salalo salalo yatashi yafita adakin, dakinsa yakoma ya kwanta yana tunanin, wai maiyasa bintu take mishi kwarjini ne? Meyasa idan yayi yunkurin yimata fada yake kasawa ne? Meyasa kuma yake masifar sonta? Da wannan tunanin har bacci ya kwashesa amma bai samu amsar tambayarsa ba....

Domin ci gaba da karanta littafin sai ku danna kan hoton kasannan don downloading zuwa kan wayoyinkuDOWNLOAD PDF
DOWNLOAD DOCUMENT
READ ONLINE

Monday, December 2, 2019

KULU - na Bala Anas Babin Lata

KULU - na Bala Anas Babin Lata


KULU 
littafin gwarzon marubuci Bala Anas Babin Lata
An buga littafin a shekarar 1991
Farashi 200 naira
Published at okadabooks


About book
Sankon mai gidana Abba shi ne ya soma gaishe ni a daidai lokacin da na shigo garejin akan Kawasakina maras salansa. Na je na kafe babur din a karshen gini daura da ofishin Abba. Sannan na nufi wajen da yake yana ta fama da wata tsohuwar lada. Kwanansa biyu yana aiki akanta. Amma har yau bai yi dace ya kammala gyaranta ba.
Mai gida Abba gajere ne mai kaurin jiki yana da sanko, ban taba ganin mai dogon sanko kamar nasa ba, tun daga goshi har keya, in rana ta haska shi daukar ido yake yi kamar madubi. Amma bai damu yasa masa hula ba.
Yana saye da shudiyar rigar kaki watau rigar aiki, ta yi bakikkirin da maikon mota.
“Barka da aiki Maigida.” Na gaishe shi a dai dai lokacin da na karasa wajensa. Na leka cikin injin ladar.
“Barka kadai.” Ya amsa ba tare da ya dago kai ya dube ni ba. Ya samu rabin minti yana aiki bai dago kai ya dube ni ba, sannan ya dan juyo. Da ya ganni a cikin kayan gida sai kamaninsa suka sauya. 
“Lafiya dai ince ko?” ya tambaye ni. Na ce lafiya kalau. “To yaya na ga haka? Ka makara amma kake bata lokaci. 'Ya dubeni sosai da ruwan kasar idanunsa sannan ya ce “Dahiru 'yan kwanakin nan ban san abin dake damunka ba. Baka son aiki ko kadan. Bayan shekaru biyu baya ban sanka da lalaci ba amma duk ka sauya. In ce ko ba shawarar Bimo kake dauka ba.”
Na ce. “Ko daya babu wata shawara da Bimo ya ke bani. Bana jin dadin jikina ne kurum tun daga lokacin da aka taso mu daga titin jami'ar Bayero.”
“To mene ne ke damunka, mutuwar zuciya." 
Na yi ajiyar zuciya. Sannan na sunkuyar da kaina. Don bani da abin cewa. Da ya ji ban ce komai ba sai ya ci gaba. “Dahiru gaskiya zan gaya maka in ba zaka zage ka yi aiki ba to zamu rabu.
“Ba wai ina nufin na kore ka ba, saboda mun dade tare da kai na kuma san matsayin da kake na maraici, amma bana son lalaci. Na san yanzu kasuwa ta lafa mana tun tasowarmu daga titin Bayero. Saboda haka ya kamata ka lura ka gane a matsayin da nake ciki. babu ciniki, amma wannan bai hana ni baka abin da na saba baka ba, ka san a maimakon abin da nake baka ba wani abu nake so ba face aiki tukuru.”
Ya sunkuya ya dauki sufana da ke yashe a kasa a gabansa. “Bimo kanina ne, amma saboda rashin aikinsa da yawan makararsa dole ne mu rabu, nan ba da dadewa ba, saboda haka ka mayar da hankali, na kara jaddada maka ka mayar da hankali ga aikin nan, don kuwa da aikinka na dogara. Ya kamata mu sake fito da sunan garejin nan” Ya koma ga aikinsa. “Jeka ka shirya ka fito aiki.”....

DOMIN CIGABA DA KARANTAWA SAI KU SIYA LITTAFIN AKAN 200 A OKADABOOKS TA HANYAR DANNA MABALLIN PURCHASE AT OKADABOOKS DAKE ANAN KASA

PURCHASE @ OKADABOOKS
DOWNLOAD NOW

Sunday, December 1, 2019

TARIHIN KASAR NUFE

TARIHIN KASAR NUFETARIHIN KASAR NUFE
Na Sadik Tukur Gwarzo
Farashi 200 Naira
About book
KASAR NUFE TANA DA DUMBIN TARIHI, KUMA CIKE TAKE DA LABARU MASU BAN MAMAKI DA KARIN ILIMI. DON HAKA LITTAFIN YA HAKAITO WASU ABUBUWA NE DA SUKA FARU NA TARIHI TUN DAGA KAFUWAR TA HAR ZUWAN FULANI HADE DA TARIHIN MANYAN MASANA KUMA MAYAKAN TA WATAU MALLAM ABDURRAHMAN DA MALLAM DANDO

Jajirtacce kana gwarzon marubucin tarihinnan ne dai SADIK TUKUR GWARZO ya rubuta, 

Zaku mallaki wannan littafi ne da naira 200 a shafin okadabooks ta hanyar danna bakin maballin download dake a nan kasa

Ga wayanda basu san yadda ake siyan littafi a okadabooks ba sai suyi mana magana ta comment muyi masu bayani


PURCHASED AT 200

SIYA LITTAFIN AKAN 200

Thursday, November 28, 2019

DAGA TAIMAKO complet

DAGA TAIMAKO complet


Daga Taimako; littafin gwarzuwar marubuciya SADNAF

Littafin yana wa'azantarwa ne akan wulakanta mutane gamida sanin darajar dan Adam da mutum ta shi

Hakanan littafin ya tabo bangaren nishadi yadda marubuxiyar tayi amfani da kwarewa ta wurin sakala cunkun nishadi wanda ko tantama banayi muddin ka karanta ko kika karanta littafinnan tofa sai kun dara

To kada dai na cika ku da surutu ga kadan daga cikin littafinWata matashiyar buduruwa na hango   a zaune akan tabarma,tana ta guga,dagani kayan mijinta take gogewa Muhibba kenan,wacce bata fi wata Biyar da aure ba,gidanta madaidaicin gida ne,dan wanda take aure ba mai k'arfi bane,Palo d'aya ne da d'akuna biyu,sai kitchen da toilet,Mijinta Abdulmajeed Mallamin Makarantar primary school ne,dai dai gwargwado suna cikin rufin asirin Allah,auren soyayya suka yi,Muhibba tana da kirki sosai ga kyauta,tsafta awajenta ba a magana,Dan inka shiga gidanta kamar karka fito sabida kamshi da tsafta da gidanta ke dashi,kayan mijinta data wanke take gogewa taji ana kwankwasa gidan,d'aga murya tayi tace "Waye"? Ji tayi an k'ara kwankwasa wa batare da anyi magana ba,mik'ewa tayi ta nufi k'ofar Dan taga wa ke kwankwasawa,doguwar Riga ce a jikinta tayi parking ba dankwalli akanta,daga bayan k'ofar ta Dan tsaya ta bud'e k'ofar tana leko da kai Dan taga waye, wani irin fad'uwa gabanta yayi jikinta ya d'au rawa sakamakon tozali da tayi da wata farar mata mai tsayi,idonta manya manya girmansu ya wuce misali,tsayinta ma yayi yawa, farinta wani irin d'aukar ido ya ringayi,gashin girar ta jajaye,haka ma leb'enta,murmushi wanan matar tayi mata tace"kiyi hakuri na zo na takuraki da kwankwasa k'ofa Dan Allah fitsari ne ya matseni shine nakeso ki taimaka min inyi dan bansan kowa anan ba," Muhibba tunda tafara magana gabanta ya tsananta fad'uwa ta kuma kasa addu'a dan matar yanayinta abar tsoro,Dan zata iya cewa tunda take ba ta tab'a ganin mai irin tsayinta ba,d'aurewa tayi tace cikin rawar baki " lah bakomai shigo kiyi" da sauri matar ta shiga ciki,ta tsaya atsakar gida,Muhibba kuwa kamar tabar gidan da gudu Dan wani irin tsoro ne ya rufeta,gashi tana so tayi addua ta kasa,d'aurewa tayi ta shiga tayi hanyar da band'akin yake tace mata  "bismillah  ga band'akin akwai ruwa aciki" gani tayi matar ta nufo ta kamar ba tafiya take ba turota ake, ware ido tayi tana kallonta cikin tsananin tsoro da tashin hankali,dasauri tabi k'afarta da kallo taga babu alamar k'afa illa ma doguwar Riga dake jikinta kawai dake Jan kasa,jikinta ne ya d'au rawa kafin tayi yunkurin yin wani Abu wuf matar ta shige band'aki ta rufo k'ofar,"innalillahi wa inna ilaihi rajiun" muhibba tace cikin tsananin tsoro da fad'uwar gaba hanyar waje tayi da sauri taje ta tsaya daga bakin k'ofar tana kallon band'akin shiru shiru matan nan bata fito ba,tsoro ne ya k'ara rufe Muhibba ta d'aga murya tace " Baiwar Allah har yanzu baki gama ba" shiru taji,ba ayi magana ba,hakan ne yasa tayi waje da gudu ta nufi gidan dake kallon gidanta,gidan surayya makociyarta ce suna mutunci sosai da ita,bubuga gidan taringayi da sauri tana kallon gidanta,Surayya kin bud'e k'ofar tayi sai data ce "Muhibba kin tabbata kece"? " nice mana yi sauri ki bud'e min"bud'ewa Surayya tayi ahankali ta leko da kanta itama kana ganinta kasan a firgice take,da sauri Muhibba ta shige kafin tayi magana surayya tace " kema kinganta ko" ? Cikin tsananin tsoro Muhibba tace wacece"? Cikin sauri tace " bakiga wata farar mata mai kama da aljana ba,gidan nan tazo wai na taimaka mata fitsari takeji tuni na rufo k'ofata dan wlh baki ganta ba kamar ba mutum ba" tunda surayya tafara magana jikin Muhibba yafara rawa gabanta in banda fad'uwa babu abinda yakeyi d'aurewa tayi tace " Innalillahi wa inna ilahi rajiun Surayya na shiga uku na lalace,wlh tazo gidana tunda ta shiga band'aki taki fitowa har yanzu, nashiga ukuna D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO zan janyo wa kaina balai Dan Allah zoki rakani inga mai take yi a band'aki tunda zu,Wani irin tsalle surayya ta buga tayi gefe tace " wa tab bazan iya rakaki ba,wane tsautsayine ya kai  ki kika barta ta shigar miki gida,wlh wanan da gani ba mutum bace Aljana ce," ai tun kafin Surayya ta rufe bakinta,Muhibba ta d'ora hannu aka taringa kuka tana ta shiga uku ta lalace " Yanzu surayya ya zanyi wlh tana cikin band'aki har yanzu bata  fito ba," sallati Surayya tayi tasa hijabinta tace "muje in rakaki Allah yasa ba aljana bace.


TOH DOMIN KARANTA CIKAKKEN LITTAFIN SAI KU DOWNLOADING NASHI A NAN KASA
👇👇👇👇👇👇👇👇👇

DOWNLOAD NOW
PURCHASE AT OKADABOOKS
DOWNLOAD PDF
DOWNLOAD DOC
DOWNLOAD TXT 

Saturday, November 23, 2019

Tuesday, November 5, 2019

MAKWABTAKA complet

MAKWABTAKA complet


MAKWABTAKA 

Littafin Makwabtaka ya samu rubutune daga jaruma kuma hazikar marubuciya da aka dade ana damawa da ita a harkan rubutu jamila umar tanko

Littafin ya dauko labarin wata yarinyace da rayuwarta ya shiga cikin wani hali a sakamakon makwabtaka, makwabataka shine abun da ya rusa mata rayuwa,ya rabata da yan uwanta,mijinta farin cikinta gamida jin dadinta wannan dalili ya sanya tayi matukar tsanar makwabtaka, 

Ana cikin hakanne rannan sai makwabtaka ya sake kwankwasa wa rayuwarta kofa a lokacin data nesanta kanta da kowa, sai de a wannan lokaci MAKWATAKAN ya zo matane cikin wani irin yanayi na musamman

Shin a tunaninku zata amince ta sake yin makwabtaka kuwa, yaya rayuwarta zata kasance 

Download the book below


DOWNLOAD NOW PURCHASE AT OKADABOOKS DOWNLOAD TXT FORMAT DOWNLOAD PDF FORMAT DOWNLOAD DOC FORMAT

Friday, October 18, 2019

GOBE JAR KASA 1 complet Shafi'u dauda giwa

GOBE JAR KASA 1 complet Shafi'u dauda giwa


GOBE JAR KASA
Littafin fasihi kuma hazikin marubuci shafi'u Dauda giwa

Littafin ya magantu ne akan wasu gwalagwalai da wani rikakken barawo ya sata ya boye babu yadda yansanda basuyi da shi ba don ya fada masu inda ya boye gwala gwalan amma na tsohon mai suna NALAMMA yaja tunga ya kafe yaki fadin inda ya boyesu,

Bayan shekaru da dama a lokacin an tura nalamma gidan jarun, harya tsufa acan rannan sai rashin lafiya ta kamashi akai maza aka garzaya asibitin cikin gari da shi

To anan nefa wasu rundunar yan fashi sukai muguwar artabo da yansanda kana suka karbi tsoho nalamma don ya fadi masu inda ya boye gwalagwalen daya sata ahekarun baya,

Shiko tsoho nalamma yaki fadamasu to ashe dai lokacin da aka kwantar da nalamma a sibiti yafadi wa wata nurse inda gwala gwalen suke ita kuma ta dau saurayinta mai suna nura suka nufi wurin bayan sun samu gwala gwalan ne NUra yai niyyar kashe budurwartasa inda ya bita da diga yana kokarin buga mata duk dan ya mallake dukiyar gaba daya.

Wayannan gwala gwalai sunyi sanadiyar MUTUWAR mutane da dama, sun shiga hannun mahandama da dama kuma sun fita,sun shiga hannun maciya amana da dama kuma sun fita,,,

Shin au waye zasu samu nasaran mallakar gwala gwalan nan

Wannan amsa zaku jita ne a cikin littafin nan mai suna GOBE JAR KASA

Sai ku downloading littafin a nan kasa

KU DANNA KAN HOTON KASANNAN DON KARANTA LITTAFIN 👇👇👇👇👇👇👇👇👇


DANNA NAN DOMIN DOWNLOADING

Monday, October 14, 2019

BIRNIN AZZALUMAI 1-5 PDF

BIRNIN AZZALUMAI 1-5 PDF


BIRNIN AZZALUMAI littafi na daya zuwa na biyar PDF

A baya mun kawo maku na hudu zuwa na shida PDF
To yanzu ga littafin nan tun daga na daya sai ku downloading nasu cikin kwnciyar hankali

Book 1

DOWNLOAD BOOK 1
Book 2


DOwnload book 2 Book 3


download book 3
Book 4

download book 4
Book 5

download book 5
Yauwa masu kukan baya download ko kuma sun kasa download dun Allah ku runga ajjiye comment akasan littafin da baya downloading don mu gyara bawai ku runga kirana ba,
Don ko kun kirani bazan saurareku ba
Shuraih Usman
08140419490

Thursday, October 10, 2019

download - KAMAR SUCE DAYA 1 DOC

download - KAMAR SUCE DAYA 1 DOC


KAMAR SUCE DAYA 1 document


Kamar suce daya littafin Asma baffa 
Wannan document din littafi na daya 1 ne zan ku download nashi ku more ina nan zuwa maku da littafi na biyu 2 shima document ne 

Kada dai ku manta documents sun fi budewa a Android da blackberries don kufara dauko reader nasu tukun kafin ku download na littafin 

Dun Allah duk wayanda suka gagara download suyi min ta comment su ajjiye min comment a kasa ni kuwa zan basu direct link din, kada wani ya kirani ko ya turomani message akan ya gagara download bazan respond ba , ku ajjiye min comment kawai,


KU DANNA BLUE DIN MABALLIN KASANNAN DON DOWNLOADING NA LITTAFIN 


KU DANNA KAN HOTON KASANNAN DON KARANTA LITTAFIN 👇👇👇👇👇👇👇👇👇


DOWNLOAD THE EBOOK NOW
Shuraih Usman 99%
08140419490

Saturday, October 5, 2019

download - KARAGAR MUKI 1 complete PDF

download - KARAGAR MUKI 1 complete PDF


KARAGAR MULKI 

LITTAFI NA DAYA 1

COMPLETE PDF

NA Abdulaziz sani m giniDOMIN DOWNLOAD NA LITTAFIN ZUWA KAN WAYOYINKU SAI KU DANNA HOTON KASANNAN 👇👇👇 👇👇 👇👇 👇

DOWNLOAD NOW

Thursday, September 26, 2019