Showing posts with label fiction. Show all posts
Showing posts with label fiction. Show all posts

Saturday, November 23, 2019

Friday, October 18, 2019

GOBE JAR KASA 1 complet Shafi'u dauda giwa

GOBE JAR KASA 1 complet Shafi'u dauda giwa


GOBE JAR KASA
Littafin fasihi kuma hazikin marubuci shafi'u Dauda giwa

Littafin ya magantu ne akan wasu gwalagwalai da wani rikakken barawo ya sata ya boye babu yadda yansanda basuyi da shi ba don ya fada masu inda ya boye gwala gwalan amma na tsohon mai suna NALAMMA yaja tunga ya kafe yaki fadin inda ya boyesu,

Bayan shekaru da dama a lokacin an tura nalamma gidan jarun, harya tsufa acan rannan sai rashin lafiya ta kamashi akai maza aka garzaya asibitin cikin gari da shi

To anan nefa wasu rundunar yan fashi sukai muguwar artabo da yansanda kana suka karbi tsoho nalamma don ya fadi masu inda ya boye gwalagwalen daya sata ahekarun baya,

Shiko tsoho nalamma yaki fadamasu to ashe dai lokacin da aka kwantar da nalamma a sibiti yafadi wa wata nurse inda gwala gwalen suke ita kuma ta dau saurayinta mai suna nura suka nufi wurin bayan sun samu gwala gwalan ne NUra yai niyyar kashe budurwartasa inda ya bita da diga yana kokarin buga mata duk dan ya mallake dukiyar gaba daya.

Wayannan gwala gwalai sunyi sanadiyar MUTUWAR mutane da dama, sun shiga hannun mahandama da dama kuma sun fita,sun shiga hannun maciya amana da dama kuma sun fita,,,

Shin au waye zasu samu nasaran mallakar gwala gwalan nan

Wannan amsa zaku jita ne a cikin littafin nan mai suna GOBE JAR KASA

Sai ku downloading littafin a nan kasa

KU DANNA KAN HOTON KASANNAN DON KARANTA LITTAFIN πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡


DANNA NAN DOMIN DOWNLOADING

Wednesday, July 17, 2019

HATSABIBIN BOKA complet

HATSABIBIN BOKA complet


HATSABIBIN BOKA
complet
Na Gentle lady

Domin karanta littafin ko download nashi sai ku danna hoton dake kasannanπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

Kadan daga ciki
Lubcy tayi ihun murna tarungume heelin"" aranar tasanarda su anisa ranar weekend sukashirya sai taraba acenne garinsu heelin Amman basuje gidansu heelin ba suka samu hotel sukahuta anan"" anasoma kiran magrib sukafita zuwa dajinda yake

Cikin kauyen taraba yake"" ka idar zuwa wajensa"" inrana tayi tsaka harzuwa dare"" tundasukashiga jejin jikinsu lubcy yasoma rawa fitiluni gasunan cikin jejin suna reto kuma ba daure sukeba basu sama basu kasa"""

Gabadaya ajikin heelin suka labe bakin wani katon iccen kuka suka iso"" kasansa anzagayeshi da karaa saman karan lullube sukeda fatuu Na namun jeji"" babu alamar kofa awajen heelince tasoma wadansu suruttai na gwalamniya"" tana kiran sunansa *hatsabibin boka*  take dajin ya amsa kuwa"" takesu lubcy sukasaki fitsariii ganin wutaa Yakama bakin wajen balbal kaitsaye heelin taja hannun lubcy tatuΓ±kΓ ri kofar"""

Aikuwa lubcy tadaddage zatafasa ihu saidaime jitayi muryanta yadisashe"" heelin tasake jawo hannunta tana tirjewa sukashigΓ  tacikin wutar"" saigasu cikin daki maigirman gaske"" su anisa sunawaje jikinsu na kyarma kowacce tacika wandonta da fitsari
Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠chapter 16
      Publish at www.hausaebooks.com.ng 
Gentle LadyπŸ’ƒπŸ½Jira suke kawai ace kat su yanki nakare""wata tsawa aka dakamasu wacce tayi sanadin faduwarsu su uku duka asome""

Heelin da lubcy suna samun kansa cikin babban dakin"" saiga wata shimfida kamar tabarmar kaba"" tataso zuwa indasuke tashimfida kanta"" batareda wani tsoroba heelin taja hannun lubcy zuwa saman shimfidar cikin tsoro tazauna gefe zaunawarsu yayi daidai dazubesu aneesa saman shinfidar take kuma suka farfado tamkar wadanda aka watsawa ruwa""
Nanfa suka soma kallon kallon aneesa tasoma kuka"" Dan tarigada ta sadakar mutuwarsuce tazo

Dukansu arikice suke inka debe heelin wacce ko ajikinta da alamu Sam batadamu dakomaiba dantasaba "" wata rikitacciyar tsawa akasaki"" tayi tartso"" bakin bishiyar yasoma cidawutaa tareda wani kugiii

Yan hanjinsu lubcy har motsi sukeyi""" tsawar tacigaba da hauhawa tareda darewar katuwar bishiyar kukar zuwa gida biyu"" wata kujerace tafito zuwa daidai kusa dasu lubcy tatsaya chak"""

Kafin kiftawar ido wata guguwace mai karfii tataso wacce tasaka gabadaya wajen yahautsine baka iyah ganin komai wannan karon ba su lubcy ba hatta heelin saida ta kare fuskarta datafin hannuwanta"""

Su lubcy kuwa gabadaya suka kankame  junansu jikinsu yana kyarma  tamkar mazari"""tsayin mintuna biyar komai nawajen yakoma kamar yanda yake kurar wajen talafa saiga *hatsabibin boka* ya bayyana asaman kujerar""

Heelin ce tafara zungurarsu lubcy dukansu suka"" bude idonsu""  wani gabjejen mutum sukayi arba dashi Wanda basutaba ganin koda maikamadashi ba acikin duniya wannan zaifikyau akirashi da dodo

Kaiyamafi dodo muni saboda katone majiyi karfii yanada damatsa manya manya tamkar irin namasu danbe""" kowanne damtse nashi daure yake dalayu nafata dakuma wani kambum karfee

Kafarsama haka""" baya sanye dariga"" cikinsa dame yake Amman kanaganin gurayenda yatara ajikinsa""" yanada tsayi sosai dantsayinsa zaiyi kamu ashirin"" kirarsa tamkar Wanda yayi alaka da samudawa""

Bakine wuluk tamkar bakin kwalta bakaganin komai afuskarsa sai jajayen idanuwansa"" kowanne mutum tsakiyar idonsa bakine ammanshi kuma zaibarda take zakiyar idonsa"" farace tass saikuma ja azagaye da itah"""

Idan yadaga ido gabadaya"" farin facewa yakeyi "" saidai ja yamamaye gurbin ido"" sumar kansa tanada yawa Wanda yawanta yasa tazubo har akan faffadan kirjinsa tayiwa mummunar fuskarsa inuwa wannan mutum dazaifito waje babu shakka dayawa mutane zasurasa rayuwarsu sanadin yin Arba da mummunar fuskarsa mai kamada ta dodanni""

Tsayawar guyuwar keda wuya yakece dawata mahaukaciyar dariya wacce tasaka dajin gabadaya ya amsa kuwa"" yadauki tsayin mintuna biyar yana wannan dariyar dagabisani yamurtuke fuska tamkar Wanda baitaba dariyaba"" heelin tabuda baki tasoma jero masa kirari"" Saikai takadiri kuma gagare kigudu sagudu sa abokan gaba sugudu"""

Turmin karfe kake shakwaramniya""" Saikai *hatsabibin boka* sugaban duk wani tantirin ajani"" komai Tsagerancin   aljani idan yazo gabanka dole yaduka nasaramaka uban maza uban hatsabibai maidakawa maza gumbaa"""  take yasake kecewa dawata mahaukaciyar dariyaaa 

Heelen tasake buda baki  daniyar magana yadaga mata hannu

Yace kafin kice wani Abu inaso insan kokin sanardasu dukokinmu dakuma sharadin mu??? Cikin saurii tace nafadamasu yasarkin bokayen duniyaa

Yagyada kansaa duk dahaka zansake sanardasu dangudun kuskure dakuma fadawa hafushinmu""" kusanii akwai sharadiii guda biyar wadanda zanfadamaku

Inhar kuka kiyaye kuntsira sharadi nafarko"" ma abota sallah basa shigowa fadataa""" duk ranarda zakuzo inda nake karwacce takuskurah tadorah goshinta akasa""

Sharadi nabiyu"" karwacce takuskurah tabada sadaka!! Domin yanadaya dagacikin abunda zaibata aikina"""

Doka ta uku muddin kika fara aikidani babuke basake zuwa wajen wani bokan "" yinhakan kuwaa zaijanyomaki masifa da bala.i dagake harbokan nakii

Sharadi nahudu duk abunda akace kikawo karkitsaya musu ko gardamΓ  idankuwa  kikatsaya watamagana take bakaken aljanu zasu zuke jininki

Doka tabiyar wajibine idan akabaki Abu dole ki aikata idankuma kinki to zaijuye zuwa kankiii""" sannan kuma duk abunda kukagani anan karkutaba idankun kiyaye kuzauna lafiyaa

Tunsa inda yasoma wannan jawabin jikinsu sadiya yasoma kyarma dama yalafiyar kurah kowaccensu tayi danasanin zuwa wajen 
yanagama rattafo sharadansa saisuka fara kallon kallo atsakaninsu gabadaya idonsu yaraina fata""

Lubcy tanason yin magana babu halii "" saida yabata izinin magana cikin sauri tace"" dama dama munasone mudanyi shawara

Batagama rufe bakintabΓ  yadakamata wata razanan nar tsawaa wacce tasaka lubcy tayi danasanin maganar

Hatta dakin saida ya amsa kuwaar yace bakuda wannan damar kusani kafin azonan akeyin shawaraa basai anzobaa danhΓ ka Ku kiyaye!!!.......... 

Domin cigaba da karanta littafin sai ku danna kan hoton dake kasannan ko sama πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

Saturday, July 13, 2019

ZAYYANA 1 & 2

ZAYYANA 1 & 2ZAYYANA
littafi na daya dana biyu  a hade
Na Nazir Adam salih
2008

Domin karanta littafin sai ku danna hoton dake kasannan πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡


Kadan daga ciki

Kada ki damu idan bakya son zuwa yanzu maje
watarana kabir yace da ita cikin sauri shi a haukansa
ya dauka abinda yace ne ya birkita kamanninta.
Farida ta gyada kai babu magana idanunta zuru akan
zanen fulawar dake kan kumatunsa.
Ganin haryanzu batayi fara'a ba sai kabir ya rankwafa
jikinta yana cewa haba farida....kiyi min murmushi
mana konaji dan dadi dadi yana gama fadin haka sai
ya zura hannayensa ya tallafo kanta sannan ya tura
bakinsa gaba da nufin zai sumbaceta anan ne to wani
abu mai kamar hannu ya zuro cikin motar kamar
daga sama ya kifawa Kabir Mari.
Wayyo Allah... Kabir yasa ihu sa'ar da yaga wani
haske kamar wuta ya gifta akan fuskarsa.
Wayyo... Wayyo dan Allah ki taimakeni za'a kasheni
kabir ya sake kwala ihu sannan a rude sai ya bude
kofar motar ya fada kasa yana birgima afilin ajje
motoci na jami'ar bayero.
Daga yau ka sake lalata ya'yan mutane dan banza
lalatacce an fadama matata irin matan da zaka iya
tabawa ce.
Wata kakkausar murya tace daga sama sannan sai
aka kece da kakkausar dariya.
Tsananin kaduwa da tsoro su suka hana farida yin
motsi tana nan zaune akan kujerar motar kamar
gunki tana hangen kabir yana ta murkususu adaidai
lokacin ne to ta lura da wasu fararen abubuwa masu
kama da kashi akan cinyarta hannunta na rawa farida
ta dauki fafaren abubuwan. Saida ta kura musu idanu
sannan ta gane ashe Hakoran mutum ne guda uku
wannan shiya sata bude kofar motar ta fice aguje
sannan tasa kabir agaba ta fara Ihu.
Nan da nan gurin ya cika da dalibai hadiman jami'ar
masu gadi da shara aka zagaye kabir an rasa mai
taba shi can sai wani kakkarfan dattijo mai shara ya
matso ya tashi kabir da kyar daga kan fuskarsa jini na
zuba nan da nan daliban dake zagaye dashi suka rike
numfashi a razane sa'ar da sukaga bakin Kabir ya
karkace ya koma baya gashi babu hakoran gaba.
Ku kamamin mu shiga dashi cikin makaranta ayi
masa addu'a ina zaton aljanu ne suka shafe shi.
Dattijon yace

Domin cigaba da karantawa sai ku danna hoton dake kasannan πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

ga duk wayanda suke samun matsala ta wurin downloading ebooks namu kuma suke da bukatar mu rubuta masu copy din littafin mu turo masu ta whatssap ko profile nasu
SAI KU TUNTUBI mamallakin shafin Shuraih Usman
Ta facebook profile nashi
Kota nambar waya 08140419490
Kota adireshin Email
shuraihusman@gmail.com
Sai de ku sani wa hakan zamu cajeku wasu kananan kudade
its Shuraih Usman 99%


Saturday, April 27, 2019

Friday, April 19, 2019